✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An gano karin gawarwakin fasinjojin da kwalekwale ya nutse da su a Neja

Wadanda aka gano gawarwakinsu sun hada da Kabawa biyu da ’yan Jihar Neja

Adadin gawarwakin da aka gano bayan nutsewar wani kwalekwalen fasinja a Jihar Neja ya karu zuwa bakwai.

Hukumar Agajin Gaggawa ta Jihar (NSEMA) ta ce an gano karin gawarwaki uku daga cikin fasinjoji 24 da kwalekwalen ke nutse da su.

A ranar Litinin da dare jirign ya nutse da fasinjojin a hanyarsu ta zuwa Karamar Hukumar Yauri ta Jihar Kebbi daga kauyen Agwara da ke jihar Neja, sai ranar Talata da yamma masu aikin ceto suka gano gawarwakin.

Shugaban Hukumar NSEMA, Garba Salihu ya shaida wa wakilinmu a ranar Laraba cewa wadadanda aka gano gawarwakin nasu da suka hada da ’yan Jihar Neja mutum biyar da kuma kuma Kabawa biyu.

Shugaban hukumar ya ce ana ci gabada aikin ceto domin gano sauran wadanda iftila’in ya ritsa da su.