✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An gurfanar da matashi kan satar babura 40 a Ondo

Matashin ya musanta zargin da ake tuhumarsa.

An gurfanar da wani matashi a Kotun Majistare mai zamanta a Akure, babban birnin Jihar Ondo kan zargin satar babura 40 wanda kudinsu ya kai Naira miliyan 10.8.

Ana zargin matashin da aikata laifin tun a watan Maris na 2021, tuhumar da ya musanta.

Dan sanda mai gabatar da kara, Sufeto Augustine Omheimhen, ya shaida wa kotun cewa wanda ake zargin ya hada baki da wasu da ake nema ruwa a jallo wajen sace babura mallakar wani mai suna Alaro Kasim.

Ya ce laifin ya saba wa Sashe na 383 wanda hukuncinsa ke karkashin Sashe na 390 na Dokar da ta haramta manyan laifuka ta Jihar Ondo da aka yi wa kwaskwarima a 2006.

Sufeto Omheimhen ya bukaci kotun ta adana wanda ake zargin a kurkuku sannan ta ba shi lokaci don ya tattaro hujjojinsa.

Sai dai lauyan wanda ake zargin, Olanrewaju Akinware, bai yarda da bukatar da takwaran nasa ya nema a wajen kotun ba, inda ya nemi a ba da belin wanda yake karewa.

Sai dai daga bisani, Alkalin Kotun, O.Y Yakubu, ta ba da belin wanda ake tuhuma kan naira miliyan biyu da kuma mutum guda biyu da za su tsaya masa.

(NAN)