✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An haramta wa jiragen ruwa tafiyar dare a Taraba

Masu sufurin jiragen ruwa a Taraba sun haramta tafiye-tafiye a cikin dare da kuma daukar kaya fiye da kima

A wani yunkuri na takaita hatsarin jiragen ruwa, kungiyar masu sufurin jiragen ruwa na cikin gida a Jihar Taraba ta haramta tafiye-tafiye da dare da kuma daukar kaya fiye da kima.

Hakan na zuwa ne kwanaki kadan bayan hatsarin kwalekwale biyu da suka yi ajalin mutum sama da 30 a makwabciyarta, Jihar Adamawa.

Shugaban kungiyar, Jidda Maoreneyo ya bayyana tafiyar dare da kuma daukar kaya da suka wuce misali a matsayin manyan sabubban hatsarin jiragen ruwa.

Ya ce a yayin da daukar kaya fiye da kima kan jawo kifewar kwalekwale, gudanar da aikin ceto a cikin duhu yana da matukar wahala, wanda ke zama silar asarar rayuka.

Don haka ya ce kawar da wadannan matsalolin biyu ya zama dole, domin rage aukuwar hatsarin kwalekwale matuka.

Ya bayyana cewa hukumar kula da ruwa na cikin gida (NIWA) ta taimaka wa mambobinsu da rigunan kariya.

Ya ce hukumar tare da ta Agajin Gaggawa ta Kasa (NEMA), da ta kashe gobara ta kasa (FFS) suna wayar da kan jama’a kan muhimmancin bin matakan kariyar tafiya a jirgin ruwa da nufin rage haddura.

Aminiya ta kawo rahoton yadda hadduran jiragen ruwa suka yi sanadin mutuwar mutum samda da 930 a cikin shekaru uku da rabi da suka gabata a Najeriya.