✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An kama shugaban makaranta kan yi wa yarinya fyade a Adamawa

Wanda ake zargin mataimakin shugaban wata makaranta ne, kuma ya yaudari yarin ya dauke ta zuwa wani kangon gini ne ya yi lalata da ita.

’Yan sanda a Jihar Adamawa sun cafke wani mutum mai shekara 52 kan zargin yi wa wata yarinya mai shekara 13 fyade.

Sanarwar da mai magana da yawun ’yan sandan jihar, SP Suleiman Nguroje, ya fitar ta nuna lamarin ya faru ne a yankin Jabbi Lamba cikin Karamar Hukumar Girei ta jihar.

Sanarwar ta ce, wanda ake zargin shi ne Mataimakin Shugaban Makarantar Sakandare ta Mata (GGSS) a Karamar Hukumar Song da ke jihar.

Ta kara da cewa, “Wanda ake zargin mazaunin Gidan Salama ne a Sangere, Jabbi Lamba a Karamar Hukumar Girei.

“A ranar 15 Nuwamba ya yaudari yarinyar zuwa wani kangon gini sannan ya yi lalata da ita.

“Mahaifiyar yarinyar ce ta kai rahoton faruwar lamarin ga ofishin ’yan sanda da ke Jabbi Lamba.”

(NAN)