✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kashe dan kasuwa bayan biyan fansar N5m a Sakkwato

’Yan bindigar da suka sace wani attajirin dan kasuwa, Alhaji Rabi’u Amarawa ranar Litinin a Jihar Sakkwato, sun kashe shi bayan karbar kudin fansa na…

’Yan bindigar da suka sace wani attajirin dan kasuwa, Alhaji Rabi’u Amarawa ranar Litinin a Jihar Sakkwato, sun kashe shi bayan karbar kudin fansa na Naira miliyan biyar.

A cewar wata majiya ta ’yan uwansa, an kashe dan kasuwar ne bayan biyan kudin fansa na naira na miliyan biyar.

“Mun samu tabbaci game da labarin mutuwarsa, kuma yanzu haka mutanenmu sun shiga daji domin dauko gawarsa,” a cewar majiyar.

Sai dai yayin da wakilanmu suka tuntubi Kakakin rundunar ’yan sandan Jihar Sakkwato ASP Sanusi Abubakar, ya ce ba shi da masaniya a kan lamarin.

“Amma zan tuntuba domin tabbatar da ingancin rahoton sannan na waiwayeku,” in ji ASP Abubakar.

Aminiya ta ruwaito cewa mutum 12 ne suka rasa rayukansu yayin da suka fita ceton dan kasuwar da ’yan bindiga suka sace a garin Amarawa da ke Karamar Hukumar Illela ta Jihar Sakkwato.

’Yan bindiga sun harbe mutanen ne yayin da suka yi yunkurin ceto wani attajirin da aka sace a gidansa da Asubahin ranar Litinin.

Wasu ’yan uwan wanda aka sace ne suka ankarar da ’yan bijilanti inda suka hada kai suka bi sahun ’yan bindigar a kokarinsu na ceto attajirin.

Aminiya ta samu cewa ’yan bindigar babu wata-wata suka bude wuta a kan mutanen da suka fita aikin ceton, lamarin da ya sanya 12 suka mace ciki har da wani dan uwan wanda aka tafi cetowa.

“Dan kasuwar da aka sace kawuna ne kuma wasu ’yan uwana biyu na daga cikin wadanda aka kashe yayin da suka fita tunkarar ’yan bindigar.”

“Yanzu haka bamu dade da binne mutum goma ba,” a cewar wani mazaunin yankin da ya bukaci Aminiya ta sakaya sunansa.

“Kai tsaye suka je gidansa suka dauke shi tamkar shi kadai suka kawo wa takakka.”

“Sai dai a yanzu komai ya lafa a yankin wanda ke da tazarar da bata wuce kilomita daya da garin Illela ba, sai dai kowa ya zugum ana jimami.”

Kakakin rundunar ’yan sandan Jihar, ASP Sanusi Abubakar yayin tabbatar da aukuwar lamarin, ya ce an yi asara mai girman gaske sakamakon mazauna garin basu sanya jami’ansu a lamarin ba gabanin bin sahun ’yan bindigar.

Sai dai ya ce hakan ba zai sa su yi kasa a gwiwa ba a yayin da tuni bincike ya kankama kuma sun tura rukunai biyar daban-daban wanda kowannensu ya kunshe hazikan ’yan sanda 63 a yankunan da ta’addancin ’yan bindiga ya fi kamari a Jihar.

“Bamu dade ta kadamar da rundunar Puff Ader II ba kuma gwamnati ta bamu motocin sintiri 16 daga cikin 80 da gwamnan Jihar ya yi mana alkawari,” in ji ASP Abubakar.