✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An kashe mayakan ISWAP 14, an ceto mutane 100 a Gwoza

An samu wannan nasara ce a tsakanin 19 ga watan Mayu zuwa 2 ga watan Yunin bana.

Dakarun Najeriya sun kashe mayakan ISWAP 14 tare da ceto sama da mutane 100 a wani samame da suka kai maboyar ’yan ta’addan da ke kauyukan Karamar Hukumar Gwoza ta Jihar Borno.

Dakarun runduna ta musamman ta Operation Hadin Kai sun kai samamen ne a kauyukan Amdaga, Balazola, Ndakaine, Jango, Sabah da Gobara, duk a Karamar Hukumar Gwoza ta jJihar Borno da ke Arewa maso Gabashin Najeriya.

Baya ga kashe ‘yan ta’adda 14 a yayin samamen, sun kama 15 daga cikinsu, suka kuma ceto iyalai 100 da suka hada da mata 33 da yara 67 kamar yadda RFI ya ruwaito.

Daraktan yada labarai na Ma’aikatar Tsaron Kasar, Manjo Janar Bernard Onyeuko ne ya bayyana haka a yayin da yake jawabi ga manema labarai a game da ayyukan sojin da ke gudana a yankin Arewa maso Gabashin Najeriya.

Janar Onyekuko ya ce an samu wannan nasara ce a tsakanin 19 ga watan Mayu zuwa 2 ga watan Yunin bana.

Dakarun sun kuma kwato wata mota kirar Toyota Hilux, wanda aka ce mallakin Hukumar Gyaran Hanyoyin Jihar Borno ce, wadda ‘yan ta’addan suka karbe a tsohuwar hanyar Marte tun a cikin watan Fabrairu.