✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An kubutar da mutum biyu da aka yi garkuwa da su a Nasarawa

'Yan sanda sun ce za a gurfanar da wadanda ake zargin a kotu da zarar an kammala bincike.

An kubutar da wasu mutum biyu da aka yi garkuwa da su a kauyen Jijipe, hedkwatar Karamar Hukumar Karu da ke Jihar Nasarawa.

Cikin sanarwar da ya fitar, mai magana da yawun ’yan sandan jihar, DSP Ramhan Nansel, ya ce tuni aka sada mutanen da ’yan uwansu.

Ya ce, ‘yan sandan yankin Karshi sun samu rahoto kan sace wasu masu gadi su biyu da suke aiki a wata gonar zamani.

Daga bisani, Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar, Mista Maiyaki Mohammed-Baba ya ba da umarnin a tura jami’ai suka bi sawun barayin.

Sanarwar ta ce, bayan zurfafa bincike da jami’an suka yi, hakan ya taimaka aka cafke wani da ake zargi da hannu cikin badakalar a yankin Karamar Hukumar Tafa ta Jihar Kaduna.

Ta kara da cewa, wanda aka damke ya jagoranci jami’an zuwa inda aka kubutar da wadanda aka yi garkuwar da su.

Nansel ya ce da zarar sun kammala bincike za a gurfanar da wadanda ake zargin a kotu.