✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kwace mota 10 ta gurbatacciyar taba a Kano

Hukumar Kare Hakkin Masu yin Siyayyan Kaya a Jihar Kano (KSCPC) ta kwace motoci 10 na taba sigari da wa’adinta ya kare. Mukaddashin Manajan-Daraktan KSCPC,…

Hukumar Kare Hakkin Masu yin Siyayyan Kaya a Jihar Kano (KSCPC) ta kwace motoci 10 na taba sigari da wa’adinta ya kare.

Mukaddashin Manajan-Daraktan KSCPC, Baffa Babba Dan-Agundi, ya ce an kwace gurbataccen sigarin ne a wani dakin ajiya da ke rukunin masana’antu da ke Sharada.

Dan-Agundi ya ce, “Hakan ta yiwu ne sakamakon goyon bayan da muke samu daga jama’a kan kokarinmu na raba Kano da gurbatattun kayan abinci da magunguna.

“Tun jiya (Talata) jami’anmu ke kwashe kayan (sigarin) wadanda kimarsu ta kai dauruwan miliyoyin Naira.

“Daga nan za mu shiga wasu kananan hukumomin da muka samu rahoton irin wadannan kaya a wasu dakunan ajiya.

“Mun samu hadin kan ’yan kasuwar Singa da su taimaka mana wajen ganowa da fallasa masu harkar kayan da wa’adin amfaninsu ya kare,” inji shi.

Ya kara da cewa kawo yanzu hukumar ta gurfanar da mutum hudu kan harkar gurbatattun kaya.

“Idan muka fita aiki mutane kan ba mu hadin kai, sun kuma fahimci hadarin amfani da irin wadannan kaya, har taya mu suke yi wurin loda kayan a motoci,” inji shi.