✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An rufe gidajen mai 14 a Kano saboda sayarwa a farashin da ya wuce hankali

Hukumar ta ce gidajen man da lamarin ya shafa suna sayar da man ne kan farashin da suka ga dama.

Hukumar Kula da Harkokin Man Fetur ta Kasa (NMDPRA) reshen Jihar Kano, ta rufe gidajen mai 14 bayan da ta kama su suna sayar da man a kan farashin da ya wuce kima.

Da yake yi wa manema labarai karin haske game da sintirin da suka yi ranar Alhamis, Jami’in hukumar a Kano, Aliyu Muhammad Sama, ya ce duk da dai a yanzu babu tsayayyen farashin fetur din a hukumance, amma gidajen man kan sayar da shi a farashin da ya wuce misali.

A cewarsa rufe gidajen man ya zama wajibi bayan da aka gano suna sayar da fetur tsakanin N290 zuwa N300 kan kowace lita.

Ya kara da cewa, a watan Disamban bara, hukumar ta rufe gidajen mai sama da 100 na ‘yan kasuwa saboda sayar da shi sama da farashin da hankali zai iya dauka.

Ya ce hukuncin wadanda lamarin ya shafa shi ne tarar N150,000 kan kowane famfo, sannan gidan man zai ci gaba da zama a rufe zuwa lokacin da ya amince ya sayar da fetur din a kan farashin da ya dace.

“Ba mu kai ga gurfanar da ‘yan kasuwar da lamarin ya shafa a gaban kotu ba saboda hakan shi ne matakin karshe.

“Mun dai dora musu tarar N150,000 kan kowane kan famfo, idan suka ki biya daga nan za mu dauki mataki na gaba.

“Za mu ci gaba da farautar gidajen man da ke sayar da fetur din a kan farashin da ya wuce kima,” inji Jami’in na NMDPRA.