✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An sa lokacin jana’izar Mahaifiyar Sarkin Kano

Jirgi zai kawo gawarta daga birnin Alkahira na kasar Masar.

Idan mai Duka ya nufa, da misalin karfe 11.00 na safiyar gobe Litinin ce ake sa ran za’a yi jana’izar Hajiya Maryam Bayero, mahafiyar Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero.

Masarautar Kano ce ta sanar da hakan ne cikin wani sako da ta wallafa a shafinta na Facebook sabanin sanarwar ta fitar a baya.

Sanarwar da masarautar ta fitar a baya ta ce, za’a yi wa Mai Babban Daki jana’iza da misalin karfe 4.00 na Yammacin ranar Lahadi a Kofar Kudu da ke Fadar a kwaryar birnin Dabo.

Hajiya Maryam Bayero, wadda aka fi sani da Mama, ko Mama Ode, ta rasu ne a safiyar Asabar a wani asibiti da ke birnin Alkahira na kasar Masar.

Sakataren Masarautar Kano, Awaisu Abbas Sanusi, ya ce Mai Babban Daki —mukami ne da ake ba wa mahaifiyar sarki mai ci— ta rasu tana da shekara 86.

Marigayiyar kuma ita ce mahaifiyar Sarkin Bichi, Alhaji Nasiru Ado Bayero, kuma babbar matar tsohon Sarkin Kano, marigayi Alhaji Ado Bayero kuma ’yar sarki a masarautar Ilorin.