✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An sace dan sandan da ke sashen yaki da garkuwa da mutane a Adamawa

Ana dai tunanin an sace shi ne bisa kuskure a maimakon wani attajiri.

Wasu ’yan bindiga sun sace wani dan sanda da ke aiki a sashen da ke kula da yaki da masu garkuwa da mutane a Karamar Hukumar Mayo-Belwa ta Jihar Adamawa.

An dai yi garkuwa da jami’in dan sandan ne, wanda ke aiki da rundunar tsaro ta ‘Operation Farauta’ a ranar Kirsimeti, kamar yadda rundunar ta tabbatar.

Operation Farauta dai wata runduna ce ta musamman da ta kunshi ’yan sanda da sojoji da kuma mafarauta da aka kafa a Jihar don yaki da matsalar garkuwa da mutanen da ta addabi wasu sassanta.

Sai dai wasu majoyoyi a yankin sun ce akwai yiwuwar an yi garkuwa da dan sandan ne bisa kuskure, ana tsammanin shi ne wani attajiri da suke fako a yankin.

Maharan dai sun yi wa garin kawanya a kan babura wajen misalin karfe 7:00 na yamma.

Majiyar, wacce ba ta amince a ambaci sunanta ba ta ce, “Mutumin da masu garkuwar ke nema wani attajiri ne, kuma yana da katon gida a kan babbar hanyar Mayo-Belwa zuwa Jalingo.

“Kowa ya san attajirin da yin shiga mai tsada, ta kece raini. Amma ranar sai Allah ya taimake shi bai yi irin wannan shigar ba.

“Cikin rashin sa’a, wani dan sandan kwantar da tarzoma das a wasu kaya masu tsada saboda bikin Kirsimeti ya fada komarsu. Sun zaci shi ne attajirin,” inji majiyar.

Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar, DSP Sulaiman Nguroje, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce suna na suna bakin kokarinsu wajen ceto shi da kuma kama masu garkuwar.