✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An tsawaita sassaucin dokar kulle da makonni hudu

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya amince da sake tsawaita sassaucin dokar kullen COVID-19 zango na biyu da makonni hudu. Karo na uku ke nan da…

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya amince da sake tsawaita sassaucin dokar kullen COVID-19 zango na biyu da makonni hudu.

Karo na uku ke nan da ake sake jinkirta dage dokar da yanzu ake ciki a fadin kasa gaba daya.

Sakataren Gwamnatin Tarayya kuma Shugaban Kwamitin kar-ta-kwana da Shugaban Kasa ya kafa don yaki da cutar, Boss Mustapha ya bayyana haka yayin jawabin kwamitin a Abuja ranar Alhamis.

A ranar Laraba kwamitin ya ziyarci Shugaba Buhari tare da yi masa jawabi kan inda aka kwana a kokarin da ake yi na yakar cutar.

Boss ya ce shawarar sake jinkirta dage kullen na daya daga shawarwarin da suka ba shugaban ya kuma amince da su.