✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Sakamakwon Zaben Gwamnonin Najeriya Na 2023 (Alkaluma Daga:INEC)

An taba kammala fim din Hausa mai dogon zango kuwa?

Sai dai wani abu da ya dade yana ci ma masu kallo tuwo a kwarya shi ne yadda ba a kammala fina-finan

An dade ana yin fina-finai masu dogon zango a masana’antar fina-finan Hausa ta Kannywood.

Sai dai tun bayan tabarbarewar kasuwancin masana’antar, da kuma lokacin kullen Kwarona, sai aka koma fim din a tashar YouTube masu dogon zango.

A irin wadannan tashoshin dai a kan samu masu kallo har sama da miliyan daya a mako daya, musamman a fim din Izzar So.

Sai dai wani abu da ya dade yana ci ma masu kallo tuwo a kwarya shi ne yadda ba a kammala fina-finan.

Fitaccen mai sharhi akan fina-finan Kannywood, Dokta Muhsin Ibrahim ne ya dawo da maganar.

Malamin ya wallafa a shafinsa na Instagram cewa, “Wai kuwa tunda aka fara yayin fina-finai masu dogon zango a Kannywood (a YouTube da Arewa24 da sauransu), wanne aka
taba gamawa?”

An ta ba shi amsa a kasa, sai dai a duk amsoshin da aka bayar, ba a samu cikakkiyar amsa ba.