✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An tsare magidancin da ya yi wa agolarsa fyade a kurkuku

Kotu ta tsare wani magidanci a gidan yari bisa zargin sa da yi wa agolarsa mai shekara 14 fyade. Babbar Kotun Majistaren ta ba da…

Kotu ta tsare wani magidanci a gidan yari bisa zargin sa da yi wa agolarsa mai shekara 14 fyade.

Babbar Kotun Majistaren ta ba da umarnin a tsare mahaucin mai shekara 40 ne bayan an gurfanar da shi a gabanta kan lalata karamar yarinyar.

Babban alkalin kotun, P.E. Nwaka ya ba da umarnin a tsare magidancina a gidan yarin da ke Ikoyi a jihar Legas, sannan ya dage sauraron karar har sai ranar 18 ga watan Fabrairu.

Tun da farko, lauya mai shigar da kara, ASP Thomas Nurudeen ya fada wa kotun cewa mutumin ya aikata laifin ne a watan Janairu a unguwar Ilasamaja da ke Legas.

Nurudeen ta ce yarinyar ta fada wa mai ba ta shawara a makaranta ne cewa mahaifin na ta ya lalata ta.

Ya ce mai ba ta shawara ta kai karar lamarin ga ma’aikatar matasa da ci gaban zamantakewar jihar Legas wacce ta kai ta ga ‘yan sanda.

Mai Shari’a Nwaka ya yi watsi da hanzarin magidancin cewa  kotun ba ta da hurumin sauraron shari’ar.

Laifin, in ji shi, ya ci karo da sashi na 137 na dokar manyan laifuka ta Jihar Legas, ta shekarar 2015.