✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An yi wa Sarki Abdullah II na Jordan rigakafin COVID-19

An yi wa Sarkin Jordan, Abdullah II, rigakafin cutar COVID-19 ranar Alhamis, kamar yadda Fadarsa ta bayyana. An kuma rawaito cewa an yi wa dan…

An yi wa Sarkin Jordan, Abdullah II, rigakafin cutar COVID-19 ranar Alhamis, kamar yadda Fadarsa ta bayyana.

An kuma rawaito cewa an yi wa dan sarkin, Yarima El Hassan bin Talal, da kuma Yarima Mai Jiran Gado Al Hussein, kamar yadda rahotanni suka bayyana.

Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ya rawaito cewa kasar ta Jordan ta fara wayar da kan mutane  a kan rigakafin na COVID-19 ranar Laraba.

An fara ne kuma da rukunin masu bukata ta musanman a sahun farko sai ma’aikatan lafiya dake biye musu.