✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

ASUU: An tashi baran-baran a tattaunawar Ministan Ilimi da shugabannin dalibai

Mun gani a kafofin sada zumunta, kana biki danka ya kammala karatu a kasar waje.

An tashi baran-baran a tattaunawa tsakanin Ministan Ilimi Adamu Adamu da shugabannin dalibai a Najeriya kan batun yajin aikin Kungiyar Malaman Jami’a ta ASUU a Abuja.

BBC ya ruwaito cewa daliban sun zargi Ministan Ilimi da ficewa zauren tattaunawar bayan sun gabatar da korafinsu.

A lokacin da yake jawabi, Shugaban Kungiyar Daliban Najeriya, Sunday Ashefon ya fada wa ministan cewa ya kai dansa kasar waje karatu.

Bidiyo ya nuna yadda shugaban yake jawabi da kuma yadda ministan ya bayar da amsa da ficewa daga zauren tattaunawar.

“Mun gani a kafofin sada zumunta, kana biki danka ya kammala karatu a kasar waje.

“Iyayenmu ba su da kudin kai mu kasahen waje, muna son a ware kudi domin ci gaban ilimi a kasar nan.

“Mai girma minista muna son mu koma makaranta,” kamar yadda shugaban daliban ya shaida wa Adamu Adamu.

Ministan ya ce “abu daya” da ya karba a tattaunawar shi ne batun shigar dalibai a tattaunawa da malaman jami’a, daga nan ya fice ya bar daliban a wurin tattaunawar.

Yajin aikin na gargadi na tsawo mako hudu da malaman jami’a suka shiga suna neman gwamnati ta aiwatar da yarjejeniyar da suka kulla a 2009 kan darin kudaden da ake kashewa bangaren ilimi.