✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Atiku: Karo 6 a shekara 30 na neman kujerar shugaban kasa

Fitowarsa a zaben 2023 shi ne karo na shida da yake neman kujerar shugaban kasa, wanda tun a shekarar 1993

A ranar Asabar, 28 ga watan Mayu, 2022 tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Atiku Abubakar ya zama dan takarar shugaban na jam’iyyar PDP a zaben 2023.

Fitowarsa a zaben 2023 shi ne karo na shida da yake neman kujerar shugaban kasa, wanda tun a shekarar 1993 fara hankoro.

A ranar Laraba, 23 ga watan Maris, 2022, Atiku ya yanki tikitin namen takarar shugaban kasa a zaben 2023. karkashin inuwar jam’iyyar PDP, babbar jam’iyyar adawa a Najeriya.

Takararsa tasa ta 2023 na zuwa ne shekara 30, tun bayan shigarsa harkar siyasa a 1993.

Ga abubuwan da suka faru da shi a tsawon lokacin da ya dauka ya neman kujerar shugaban kasa:

Zaben 1993

A karon farko, Atiku ya fito takarar shugaban kasa a karkashin jam’iyyar SDP a zaben 1993.

Amma ya sha kaye zaben fitar da dan takara, wanda Cif MKO Abiola da mataimakinsa, Babagana Kingibe suka samu nasara.

Daga baya gwamantin soji ta Janar Ibrahim Badamasi Babangida ta soke zaben, wanda Abiola da Kingibe suka samu kuri’a 8,341,309 (58.36%).

Zaben 2007

Atiku ya kasance mataimakin shugaban kasar Najeriya na tsawon shekara takwas (1999 zuwa 2007).

A lokacin, wasu gwamnoni sun nemi ya fito takarar shugaban kasa a zaben 2003, amma ya ce a bari sai Obasanjo ya kammala wa’adinsa na biyu a 2007, sai dai kuma kafin nan suka raba gari da uban gidan nasa.

A 2007 ya sauya sheka daga jam’iyar PDP mai mulki zuwa sabuwar jam’iyyar AC, inda ya samu tikitin takarar shugaban kasa.

A wanna karon ma ya kara shan kaye a matsayin na uku a zaben mai cike da rundani, wanda dan takarar shugaban kasar jam’iyyar PDP, Umaru Musa Yar’Adua, ya lashe.

Dan takarar jam’iyyar ANPP Muhammadu Buhari, ne ya zo na biyu, Atiku kuma ya zo na uku, a zaben da masu sanya ido na Tarayyar Turai suka ce ba su taba ganin mummunan zabe irinsa ba.

Zaben 2011

A 2011 Ya sake komawa PDP, ya nemi takarar shugaban kasa, amma shugaban kasa na wancan lokacin, Goodluck Jonathan ya kayar da shi a zaben fid dan takarar jam’iyyar.

Zaben 2015

A 2014, Atiku ya sauya sheka daga jam’iyyar PDP zuwa APC ya nemi tsayawa takarar shugaban kasa, amma Muhammadu Buhari ya kayar da shi da sauran ’yan takara a zaben fid da dan gwani.

Zaben 2019

Zuwa 2017 ya bar APC ya koma PDP, inda ya zama dan takarara shugaban kasa, amma Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya kayar da shi.

Zaben 2023

A yayin da ake shirye-shiryen babban zaben 2023 kuma, Atiku ya kara yankar tikitin takarar zaben shugaban kasa a karkashin inuwar jam’iyyar PDP.

A ranar Asabar 28 ga watan Mayu 2022, shekara daya daidai kafin karewar wa’adin gwamnati mai ci, Atiku ya lashe zaben dan kararar shgaban kasa na PDP.

Zaben 2023, shi ne karo na shida da Atiku ke hankoron zama shugaban kasar Najeirya.

Tuni dai ya bayyana wasu bangarori biyar da idan har ya kai labari a 2023 gwamnatinsa za ta mayar da hankali a kansu.

Bangarorin sun hada da hadin kan kasa, tsaro, tattalin arziki da sauransu.