✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ba na garkuwa da mutane sai dai kawai na kashe su —Aleiro

Wadannan su ne dalilan da nima ba zan bar mutane su huta ba.

Kasurgumin dan bindigar nan da a kwanan nan aka nada shi Sarkin Fulani ’Yandoton Daji, Ado Aleiro ya yi kurin cewa ba ya satar mutane ko garkuwa da su idan ya kai farmaki garuruwa.

Nadin sarautar Aleiro, wanda shi ne jagoran ’yan ta’adda a Tsafe da Faskari a jihohin Zamfara da Katsina, ya jawo ce-ce-ku-ce a fadin kasar nan.

Da yake zantawa da sashen binciken kwakwaf na BBC Africa Eagle, Ado Aleiro ya ce, “na fi karfin na sace mutane, kashe su na ke yi. Amma yara na na yin haka.”

A hirarsa da ake kyautata zaton ita ce ta farko da ya yi da manema labarai wacce aka nadi bidiyonta kuma wanda za a saki ranar 25 ga watan Yuli, Aleiro ya bayyana cewa dalilin da ya ke kashe mutane kuwa shi ne yadda ake muzguna wa Fulani makiyaya.

A cikin hirar da aka yi wa lakabi da “Mayakan ’Yan Bindiga na Zamfara”, Aleiro ya bayyana cewa ya fusata da Hausawa da gwamnatin Najeriya.

“An muzguna musu [Fulani], an yi watsi da su kamar ba ’yan kasa ba.

“Sojojin sama na kashe su sannan duk inda suke bi su yi kiwo duk an kwace, babu su yanzu.

“Wadannan su ne dalilan da nima ba zan bar mutane su huta ba.

BBC ya kuma tuntubi dan ta’addan da ya jagoranci sacewa da kuma garkuwa da daliban Sakandiren Mata ta Jangebe a Karamar Hukumar Talata Mafarar Jihar Zamfara, inda ya bayyana cewa sai da aka biya su naira miliyan 60 a matsayin kudin fansa kafin sako daliban.

Da aka tambaye shi me suka yi da kudin, sai ya ce, “Mun kara sayen bindigogi.”

A ranar Asabar da ta gabata ce Sarkin ’Yandoton Daji, Aliyu Marafa ya nada Ado Aleiro sarautar Sarkin Fulanin ‘Yandoton Daji.

Sai dai kuma kwana daya bayan nadin, Gwamnatin Jihar Zamfara ta ba da sanarwar dakatar da sarkin tare da soke nadin, sannan ta kafa kwamitin binciken yadda aka nada Aliero.

Bayanai sun ce gwamnatin Katsina da ke neman Aliero ruwa a jallo, ta tanadin bayar da tukwicin Naira miliyan 5 ga duk wanda ya bayar da bayanan da suka kai ga kama shi, wanda ake zargi da kashe mutane 52 a garin Kadisau da ke Karamar Hukumar Faskari a shekarar 2019.