✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ba sace ni aka yi ba, guduwa na yi – Amaryar Kano

Na yi hakan ne don kada a yi auren.

Amaryar da aka rika yamudidin an sace kwanaki biyu kafin aurenta a jihar Kano mai suna Amina, ta bayyana cewa kanzon kurege ne.

A jawabin da Amina ta yi wa Aminiya, ta ce ta yi hakan ne don hana auren yiyuwa saboda ba ta son mijin.

“Na yi hakan ne don kada a yi auren. Duk da cewa ni na ce ina sonsa da farko amma daga baya sai na ji ba na son sa amma na so na gaya wa iyayena amma saboda ina jin nauyinsu sai na kasa sanar da su.”

Sai dai ta nemi afuwar iyayenta da mijin nata a kan abin da ta aikata inda ta ce a shirye take a gudanar da auren a wannan lokaci saboda tana son sa fiye ma da baya.

Rundunar ’yan sanda Jihar Kano ta inganta rahoton, inda ta bayyana cewa amaryar nan da aka sanar da bacewarta yayin da ya rage kwanaki biyu ga lokacin aurenta ba sace ta aka yi ba kamar yadda iyayenta suka yi zargi, ita da kanta ta buya don hana yiyuwar auren.

Kakakin Rundunar ‘’yan sandan DSP Abdullahi Haruna Kiyawa ya bayyana cewa yarinyar ce ta kitsa guduwa inda kuma bincike ya nuna cewa a tsawon kwanaki hudu da ta yi a boye ta yi yawo wurare da dama.

“Ana nan ana gudanar da bincike game da wuraren da ta je da kuma wayar da ta yi da mutane daban- daban don haka akwai abubuwan da suka faru wanda bincike ne kadai zai nuna hakan.”

Kazalika, Kawun amaryar Gwani Rayyanuna ya bayyana cewa ya yi mamakin jin wannan magana kasancewar yarinyar da kanta ta kawo yaron har suka gai ga kulla maganar aure.

Sai dai angon Hassan Umar ya ki cewa komai a kan batun inda ya yi togarciya da cewa har zuwa wannan lokaci bai yi tozali da ita ba.