✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Bakuwar cuta ta kashe mutum 2, wasu 160 na asibiti a Kano

Mutanen na nuna alamun fitsarin jini, zazzabi, shawara da sauransu

Mutum biyu sun rasu, wasu akalla 160 kuma na kwance a asibiti a Kano bayan cin abincin da ake zargin na dauke da gurbataccen sinadarin Citric Acid.

Tuni dai gwamnatin ta haramta amfani da sinadarin kara dandano ko armashi ko tsamin abinci da kayan shaye-shaye a Jihar, saboda zargin miyagun ’yan kasuwa da sayarwa da kuma amfani da sinadarin da wa’adinsa ya kare tun shekara daya da ta gabata.

Ma’aikatar Lafiya ta Jihar Kano ta ce mutanen da suka harbu da cutar da ke kwance a asibitoci a fadin Jihar na nuna fama da fitsarin jini, zazzabi, shawara da sauransu.

Babban Likitan Binciken Cututtuka na Jihar Kano, Dokta Bashir Lawan ya ce an samu barkewar cutar a Kananan Hukumomi takwas — Gwale, Birni, Dla, Bunkure, Fagge, Gwarzo da Dawakin Tofa.

Ya ce an dauki samfurin sinadarin kara armashi da dandanon kayan shaye-shaye da wa’adinsu ya kare domin tabbatar da alakar cutar da gurbataccen sinadiri ko gubar dalma da cutar.

An kuma dauki saufurin ruwa daga wata makabarta domin tantance ko gurbataccen ruwa na da alaka da cutar da aka fara ganowa a jikin wata karamar yarinya mai shekara shida.

“Sakamakon da dakin gwaje-gwaje na kasa ya bayar ya nuna ba zazzabin Lassa ko shawara ba ce, amma muna jiran wani sakamakon mu gani ko zazzabin Dengue ne.”

Tuni dai Gwamnatin Kano ta ayyana wasu asibitoci domin jinyar wadanda suka kamu da cutar.

Asibitocin sun hada da Asibitin Koyarwa na Malam Aminu Kano (AKTH), Asibitin Kuwararru na Murtala da Asibitin Cututtuka Masu Yaduwa (IDH) wanda ka fi sani da asibitin zana.

Sauran su ne Asibitin Shaikh Muhamamd Jidda, Asibitin Shehu Waziri Gidado, Babban Asibitin Rano da asibitoci biyu a Karamar Hukumar Dawakin Tofa.

Aminiya ta ziyarci Asibitin Zana inda ta iske kimanin mutum 30 da aka kwantar saboda cutar na fama da matsanancin ciwon ciki, amai da fitsarin jini.

Hukumar Kula da Ingancin Abinci da Magunguna ta Kasa (NAFDAC) ta ce ita ma ta dauki samfurin ruwa da na sinadaren kara armashin abinci domin gudanar da gwaji bayan barkewar cutar a Kano.

Babban Jami’in NAFDAC a Kano, Shaba Muhammad, ya ce ana gudanar da gwaje-gwajen ne a Kaduna kuma ana sa ran samun sakamakon ba da jimawa ba.