✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Buhari ya karbi bakuncin Sheikh Dahiru Bauchi

Sheikh Dahiru Bauchi ya kai wa Shugaban ziyara a ranar Alhamis.

Shugaba Muhammadu Buhari ya karbi bakuncin jagoran Darikar Tijjaniya a Najeriya, Sheik Dahiru Usman Bauchi a Fadarsa da ke Abuja.

A ranar Alhamis ce babban malamin ya kai wa Shugaban ziyara a cewar wani sako da hadimin Shugaban Kasar, Mista Femi Adesina ya wallafa a shafinsa na Facebook.

Sai dai sanarwar ba ta yi wani karin bayani ba dangane da abin da suka tattauna ya zuwa yanzu.

Duk da cewa babu wata masaniya dangane da maudu’in da suka tattauna, amma rahotanni na cewa hakan ba ya rasa alaka da kisan da aka yi wa wasu matafiya a makon da ya wuce a Jihar Filato.

Cikin hotunan da hadimin shugaban kasar ya wallafa, Buhari ya karbi bakuncin Sheikh Dahiru Bauchi tare da Ministan Sadarwa, Sheikh Isa Ali Ibrahim Pantami.

Buhari tare da Sheikh Dahiru Bauchi da kuma tawagar babban malamin
Buhari tare Ministan Sadarwa Sheikh Pantami lokacin da suka karbi bakuncin Sheikh Dahiru Bauchi

Kimanin mutum talatin ne suka mutu sakamakon wani hari da ake zargin ’yan matasan kabilar Irigwe da kaiwa kan motar matafiyan a cikin birnin Jos, amma sun musanta wannan zargi.

Aminiya ta ruwaito cewa, an tare matafiyan ne a kan hanyarsu ta komawa Jihohin Ondo da Ekiti bayan sun halarci taron addinin Musulunci a Jihar Bauchi.

A biya diyyar mabiya na da aka kashe

A kwanakin bayan nan ne Sheikh Dahiru ya bukaci gwamnati ta biya diyyar mabiyansa da aka karkashe a yankin Gada-Biyu na garin Jos na Jihar Filato a ranar Asabar.

Sheikh Dahiru Bauchi wanda ya bukaci biyan diyyar daga Gwamnatin Jihar Filato ya kuma nemi a hukunta wadanda suka kashe almajiran nasa guda 30 tare da jikkata wasu da dama.

Shehin malamin, wanda Shugaban Kasa ya yi wa ta’aziyya bisa wakilcin Ministan Sadarwa, Isah Ali Pantami, ya bayyana bukatar biyan diyya ga iyalan mamatan da kuma hukunta masu laifin ne a wata zantawa da Sashen Hausa na BBC ya yi da shi.

Sheikh Dahiru Bauchi ya kuma gargadi al’ummar Musulmi da su nisanci daukar doka a hannunsu da sunan daukar fansa a kan kisan matafiyan da aka yi.