✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Buhari ya sake kiran taron Majalisar Tsaro a Abuja

Taron dai na zuwa ne a daidai lokacin da Najeriya ke fama da kalubalen tsaro iri-iri.

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya sake kiran taron Majalisar Tsaro ta Kasa a Fadar Shugaban Kasa ta Ado Rock dake Abuja wanda aka fara yi ranar 30 ga watan Mayun 2021.

Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya (NAN) ya rawaito cewa Shugaban ya kira taron ne da nufin tattauna matsalolin tsaron dake addabar kasar.

Wadanda ke halartar taron na ranar Talata kamar na makon da ya gabata sun hada da Mataimakin Shugaban Kasa, Farfesa Yemi Osinbajo da Sakataren Gwamnatin Tarayya, Boss Mustapha da Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Kasa, Farfesa Ibrahim Gambari.

Sauran sun hada da Ministan Tsaro, Manjo Janar Bashir Magashi da Mai ba Shugaban Kasa Shawara Kan Harkokin Tsaro, Manjo Janar Babagana Monguno mai ritaya da kuma Babban Sufeton ’Yan Sanda na Kasa Usman Alkali Baba.

Kazalika, Babban Hafsan Tsaron Najeriya, janar Lucky Irabor da Babban Sojin Kasa, Laftanar Janar Ibrahim Attahiru da Babban Hafsan Sojin Ruwa, Bayis Admiral Auwal Zubairu da Babban Hafsan Sojin Sama, Eya Mashal Isiaka Amao suma suna halartar taron

Taron dai na zuwa ne a daidai lokacin da Najeriya ke fama da kalubalen tsaro iri-iri.