✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Buhari ya yi sabon dogari

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya amince da nadin mataimakin Kwamishina ‘yan sanda,  Aliyu Abubakar Musa a matsayin sabon babban dogarinsa (CPSO). Nadin sabon dogarin na…

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya amince da nadin mataimakin Kwamishina ‘yan sanda,  Aliyu Abubakar Musa a matsayin sabon babban dogarinsa (CPSO).

Nadin sabon dogarin na zuwa ne bayan an sauya wa tsohon wajen aiki, kamar yadda mai taimaka wa shugaban kasa a bangaren yada labarai Malam Garba Shehu ya sanar a ranar Litinin 29 ga watan Yuni.

Ya ce DCP Aliyu Abubakar Musa ya maye gurbin CP Abdulkarim Dauda wanda aka yi wa sauyin wajen aiki.

Sabon dogarin na Shugaba Buhari, DCP Aliyu Abubakar Musa, dan asalin jihar Neja, ya yi aiki ne a rundunar ‘yan sandan a shiyya ta 5 da ke Benin, kafin sabon nadin nasa Dogarin Shugaba Buhari.