Buhari zai sake bai wa su Buratai mukami | Aminiya

Buhari zai sake bai wa su Buratai mukami

    Ishaq Isma’il Musa

Shugaba Muhammadu Buhari ya nemi Majalisar Dattawa ta amince da nadin tsaffin manyan hafsoshin soji da ya sallama a makon jiya a matsayin jakadun Najeriya.

Sanarwar hakan tana kunshe cikin wani sako da hadimin shugaban  kasar na shafukan sada zumunta, Bashir Ahmad ya wallafa da Yammacin ranar Alhamis a shafinsa na Twitter.

Hadimin shugaban kasar ya ce an aike da sunayen tsaffin manyan hafsoshin sojin da suka yi ritaya zuwa Majalisar Dattawan Najeriya da zummar nada su a matsayin jakadu ga kasar a wasu kasashe na ketare.

Malam Bashir ya ce tsaffin manyan hafsoshin sojin da da aka aike wa Majalisar Dattawan sunayensu sun hadar da Janar Abayomi Olanisakin da Vice Admiral Ibok-Ete Ibas.

Sauran sune Laftanar Janar Tukur Buratai da Air Marshal Sadique Abubakar da kuma Air Vice Marshal Muhammad S Usman.