Da dumi-dumi: Sheikh Ahmad Bamba ya rasu | Aminiya

Da dumi-dumi: Sheikh Ahmad Bamba ya rasu

    Abubakar Muhammad Usman

Fitaccen malamin addinin Musulunci a Jihar Kano, Sheikh Ahmad Bamba, ya rasu a ranar Juma’a.

Iyalan malamin, wanda ake wa lakabi da Dokta Ahmda BUK, ne suka tabbatar da rasuwarsa bayan ya sha fama da rashin lafiya.

Sheikh Bamba ya yi fice wajen gudanar da majalisin karatu inda yake gabatar da yin Tafsirin Alkur’ani da Hadisai a Masallacin Jami’ar Bayero ta Kano (BUK) da kuma makarantarsa da ke unguwar Tudun Yola.

Za a yi jana’izar malamin bayan Sallar Juma’a a da misalin karfe 1:30 na rana a Masallacin Darul Hadith da ke Tudun Yola, Kabuga a Kano.