✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Daliban jami’ar Abuja na zanga-zanga kan karin kudin makaranta

Dole ne a janye karin kudin makaranta da aka yi mana.

Daliban Jami’ar Abuja sun tare babbar hanyar zuwa filin tashi jirage na Abuja, inda suke gudanar da zanga-zanga kan karin kudin makaranta da jami’ar ta yi.

Kamfanin Dillacin Labarai NAN ya rawaito cewa, an hangi wasu daga cikin daliban yayin da suke zanga-zangar dauke da kwalaye da aka yi rubutu a jikinsu.

Oladeja Olawale, shugaban Kungiyar Daliban Jami’ar (SUG), ya bayyana cewa sai an biya bukatunsu sannan za su daina zanga-zangar.

Ya kara da cewa dole ne a janye karin kudin makaranta da aka yi musu sannan a bude shafin rajistar Intanet na Jami’ar da aka rufe.

Wani dalibin jami’ar dauke da kwali.

Olawale ya ce babbar hanyar da suka rufe ba za su bude ta ba matukar shugaban Jami’ar Farfesa Abdul-Rasheed Na-Allah, bai saurari kokensu ba.

Wasu daga cikin daliban dauke da kwalaye.

Da yake jawabi kan zanga-zangar, kakakin jami’ar Habib Yakoob, ya ce za su zauna da daliban a teburin sulhu don nemo mafita.

Zanga-zangar dai ta kawo tsaiko ga masu ababen hawa, da sauran jama’a da ke amfani da wannan hanya.