✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dalilan da Kotu ta sallami shugaban IPOB daga zargin ta’addanci

Kotu ta ce gwamnati ta aikata laifi da ta kamo Shugaban IPOB, Nnamdi Kanu daga kasar waje.

Kotun Daukaka Kara ta Tarayya ta zargi gwamnatin Tarayya da aikata laifi wajen kamo shugaban haramtacciyar kunkiyar IPOB, Nnamdi Kanu daga kasar waje domin ya fuskanci shari’a kan zargin ta’addanci.

Mai Shari’a Jummai Hanatu, ta sallami Nnamdi Kanu, duk da  zarge-zarge bakwai da gwamanti ke masa na ta’addanci, saboda kotun ba ta da hurumin sauraron shari’ar domin gwamnati ta saba dokar kasa da kasa wajen Nnamdi Kanu daga kasar Kenya zuwa Najeriya.

“Yin awon gaba da Nnamdi Kanu da karfin tsiya daga Kenya zuwa Najeriya da Gwamnatin Tarayya ta yi, karar ya saba wa dokokin kasa da kasa,” in ji Mai Shari’a Hannatu, wadda ta jagoranci wasu alkalan kotun da ke zamanta a Abuja.

Amma Gwamnatin Tarayya ta tsaya a kan bakanta, cewa ta sake kamo shi da kuma taso keyarsa daga Kenya ne bayan umarnin kotu na sake tsare shi bayan ya yi batar daba a watan Satumban 2017.

Amma lauyoyinsa suka ce, “Umarnin sake tsare shi da kotu ta bayar a Najeriya kawai za ta yi aiki ba a wajen kasar ba.”

Lauyansa, Ifeanyi Ejiofor ya sanar ta shafinsa na Facebook cewa, “Mun yi nasara, Kotun Daukaka Kara ta wanke ta kuma saki Nnamdi Kani.”

Alkalan sun kuma ce tuhume-tuhumen da hukumar DSS da Gwamantin Tarayya suke wa Nnamdi Kanu ba su da makama, saboda sun kasa gabatar da kwararan hujjoji kamar yadda doka ta tanadar.

waiwaye

Kanu ya daukaka kara zuwa kotun ne yana neman ta yi watsi da tuhume-tuhumen da gwamnati ke masa bayan Mai Shari’a Binta Nyako ta Babbar Kotun Tarayya ta soke 8 daga cikin zarge-zarge 15 da ake masa na cin amanar kasa, saboda rashin kwararan hujjoji.

Zarge-zargen da Binta Nyako ta soke sun danganci zargin sa da tunzura jama’a ta shirye-shiryen rediyo da su tayar da zaune tsaye tare da kai wa ’yan sanda hari da kuma lalata kadarorin gwamnati.

A ranar 23 ga Disamba, 2015 aka fara gurfanar da shi gaban kotu, kafin daga bisani kotu ta bayar da belinsa a ranar 25 ga watan Afrilu, 2017.

Daga baya ya saba sharadin belin nasa, ya ki zuwa halartar zaman kotu, kafin daga bisani jami’an tsaro su taso keyarsa daga kasar waje.

A lokacin da yake zaune a kasar waje, gwamnati ta zarge shi da tunzura mutane a Nejeriya su dauki doka a hannunsu.

Tserewarsa zuwa kasar waje ta sanya Babbar Kotun Tarayya yin watsi da bukatar sa na beli a watan Mayu da Yuni, tana mai kafa hujja da abin daya yi a 2017, wanda ya sanya ta ci gaba da shari’ar ba tare da shi ba.

Amma lauyansa, Mike Ozekhome (SAN), ya shaida mata cewa ya tsere a 2017 ne bayan sojojin rundunar Operation Python Dance sun kai hari a gidansa da ke Afaraukwu-Ibeku, Umuahia, a Jihar Abia, inda suka kashe mutum 28.

Ozekhome ya ce saboda haka neman belin bai saba doka ba.