Dan Majalisa na cikin masu daukar nauyin IPOB —Buhari | Aminiya

Dan Majalisa na cikin masu daukar nauyin IPOB —Buhari

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari
Shugaban Kasa Muhammadu Buhari
    Sagir Kano Saleh

Gwamnatin Tarayya na bincike kan wani dan Majalisar Tarayya da ke da hannu a ayyukan masu neman ballewa daga Najeriya.

Shugaban Kasa Muhammad Buhari ne ya sanar da hakan a jawabinsa na cikar Najeriya shekara 61 da samun ’yanci, inda ya yi kira ga ’yan kasar da su guji kalamai ko ayyukan da ke iya wargaza hadin kan kasar.

“Kamun Nnamdi Kanu da Sunday Adeyemo (Igboho) na baya-bayan nan, da kuma binciken da ake gudanarwa ya gano wasu manyan masu kudi da ke daukar nauyin ayyukan wadannan mutane; Muna kuma bin diddigin wadannan masu ba da kudi, ciki har da wani dan Majalisar Tarayya,” inji shi.

A yayin da Nnamdi Kanu da haramtacciyar kungiyarsa ta IPOB ke neman ballewa daga Najeriya ta kafa kasar Biafra, kungiyar ta sha tunzura magoya bayanta su saba wa dokokin Najeriya baya ga hare-hare da ta kai wa gine-ginen gwamnati gami da kashe jami’an tsaro da dama.

Shi ma a nasa bangaren, Igboho mai ikirarin neman kafa kasar Yarabawa zalla ta Jamhuriyar Oduduwa, ya sha tuntura magoya bayansa, har suka ba wa makiyaya wa’adin ficewa daga daukacin yankin Kudu maso Yammacin Najeriya.

A yanzu dai Kanu na hannun gwamnati yana fuskantar shari’a kamar Igboho wanda shi kuma aka kama a Jamhuriyar Benin zai tser zuwa kasar Jamus, bayan hukumomin Najeriya sun fara nemansa ruwa  a jallo.

Buhari ya ce duk da cewa gwamnati na yin iya kokarinta wajen biyan bukatun masu korafe-korafe a sassan Najeriya, gwamantinsa ba za ta yi wata-wata ba wajen murkushe masu neman tayar da zaune tsaye da masu daukar nauyinsu.

, “Gwamnatinmu za ta ci gaba da aiki kan hanyoyin tattaunawa don magance korafe-korafe, amma kuma a shirye muke mu dauki tsauraran matakai kan masu tada fitina da iyayen gidansu wadanda ke yin barazana ga tsaron kasa.

“Najeriya ta mu ce gaba daya, kuma babu wani zabi game da hadin kanta. Babbar nasararsa za ta iya samuwa ne kawai idan duk muka hada kai da manufa daya ta samun zaman lafiya da wadata ga al’ummarmu.”

“A matsayinmu na Gwamnati, a shirye muke mu kama tare da gurfanar da duk masu tayar da zaune tsaye ta hanyar kalaman ki; Kudurin mu na tabbatar da zaman lafiya, hadin kai da Najeriya daya abu ne mai dorewa.

“Yin yaki da sunan neman zaman lafiya ba ba shi ne fatarmu ba. A koyaushe za mu iya warware korafinmu cikin lumana ba tare da zubar da jini ba.

“Saboda haka ina amfani da wannan dama, a wannan rana ta musamman da ke alamta hadin kai da dunkulewar babbar al’ummarmu, don rokon dukkannin ’yan Najeriya da su rungumi zaman lafiya da tattaunawa, game da duk abin da ke damun su.

“Ana tunzura mutane su yi tashin hankali ta hanyar kalmomi. Kalaman rashin hankali na wasu kalilan sun haddasa asarar rayuka da dama da ba a ji ba su gani ba tare da lalata kadarori.”