✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dan sanda ya mayar da N1.2m da ya tsinta a Kano

Sajan din dan sanda ya mayar da Naira 1.2m da ya tsinta a wurin da aka yi hatsari.

Wani jami’in dan sanda ya mayar da Naira miliyan 1.2 da ya tsinta a wurin da aka yi hatsari a Kano.

Sajan Kabiru Isah daga shashen kula da zirga-zirga (MTD) a Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano, ya gano N1,294,200.00 din ne a yayin da yake bincike, jim kadan bayan hatsarin da ya yi sanadiyyar mutuwar mai kudin.

Wata tirela ce ta kade wani mai tuka babu, a kan titin Zaria Road, a lokacin da yake dauke kudaden da ya sanya su a cikin akwatin takalma.

Da yake mika kudin ga iyalan mamacin, Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Kano, Sama’ila Shu’aibu Dikko, ya yi kira ga sauran jami’an ’yan sanda da mutanen Kano su yi koyi da halayyar Sajan Kabiru.

Ya kuma jinjina wa Sajan Kabiru bisa nagartar da irin amanar da ya nuna.

Da yake yaba wa jami’in, Manajan Daraktan Hukumar Kula da Ababen Hawa ta Jihar Kano (KAROTA) Baffa Babba Dan Agundi ya yi masa kyautar N100,000.00.

Shi ma ya bayyana farin ciki da jami’in dan sandan inda ya ce, “Mun yaba da abin da ya yi, muka wajibi ne mu ba su (yan sandan) taimakon da suke bukata.”