✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dan wasan Real Madrid, Rafael Varane ya kamu da COVID-19

Dan wasan ya kamu da cutar COVID-19 bayan gwajin da aka masa a ranar Litinin.

Dan wasan bayan kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid dan asalin kasar Faransa, Rafael Varane ya kamu da cutar COVID-19.

An fitar da sanarwar kamuwarsa da cutar ne a ranar Talata, yayin da Real Madrid ke shirin karawa da Liverpool a wasan Cin Kofin Zakarun Turai, da misalin karfe 8 na dare.

Kamuwar dan wasan ya kawo cikas ga Real Madrid, wanda da ma can za ta buga wasan ne ba tare kyaftin dinta ba, Sergio Ramos, sakamakon rauni da ya samu a gwiwarsa.

Kazalika, Varane ba zai samu damar buga wasan El-Clasico da za a yi tsakanin Real Madrid da Barcelona ba, saboda zai killace kansa na tsawon mako biyu.

Dan wasan bai yi atisaye da ragowar abokansa ba a daren ranar Litinin, saboda jiran sakamakon gwajin da aka yi masa, wanda daga karshe ya nuna yana dauke da kwayar cutar.

Kocin Madrid, Zinedine Zidane na da damar yin amfani dan wasan baya dan asalin kasar Brazil, Eder Militao.

Madrid za ta kara da Liverpool ba tare da Varane, Ramos, Carvajal da kuma Hazard ba.