✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

De Bruyne ya sake lashe gwarzon dan wasan Firimiya

Dan wasan ya sake lashe kyautar gwarzon dan wasa a karo na biyu a jere.

Fitaccen dan wasan tsakiya na kungiyar kwallon kafa ta Manchester City, Kevin De Bruyne, ya sake lashe kyautar gwarzon dan wasan gasar Firimiyar Ingila a karo na biyu.

Dan wasan mai shekara 29, ya kafa tarihi wajen lashe kyautar  kungiyar kwararrun ’yan wasan Ingila ajin mazaa karo na biyu a jere kwatankwacin tarihin da Cristiano Ronaldo ya kafa a lokacin da yake Manchester United.

  1. An sace Hakimi da matansa biyu a Neja
  2. Ya kamata jihohin Arewa su sake fasalin nomansu — Sa’ad Gulma

De Bruyne wanda dan asalin kasar Belgium ne, ya zura kwallaye shida a bana tare da taimakawa wajen zura kwallaye 12 a raga.

Dan wasan ya taka muhimmiyar rawa inda taimaka wa kungiyarsa ta Manchester City wajen lashe gasar Firimiyar Ingila a bana.

Sai dai kungiyar tasa ta yi rashin nasara a hannun Chelsea ta ci daya mai ban haushi a wasan karshe na gasar cin Kofin Zakarun Turai.