✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dino Melaye ya sha kaye a zaben fid da gwanin Sanata a Kogi

Ya sha kayen ne a hannun wani dan Majalisar Wakilai mai ci

Tsohon Sanata mai wakiltar Kogi ta Yamma, Dino Melaye ya sha kaye a zaben fid da gwani na jam’iyyar PDP a yunkurinsa na sake komawa kan kujerar.

Sanata Dino dai ya sha kayen ne a hannun abokin takararsa, Teejay Yusuf, wanda ya sami kuri’u 163, shi kuma Dino ya sami kuri’a 99 a zaben da aka gudanar ranar Talata.

Da yake jawabi ga manema labarai bayan kammala zaben, wanda ya sami nasarar, wanda kuma dan Majalisar Wakilai ne mai ci da ke wakiltar mazabar Kabba/Bunu ya ce nasarar da ya samu ikon Allah ce.

Kazalika, ya kai ziyarar godiya da ban gajiya ga jagororin mazabar ta Kogi ta Yamma bisa gudummawar da suka ba shi a nasarar da ya samu ta zama dan takarar Sanatan a PDP.

Ya kuma yaba wa daliget-daliget na jam’iyyar bisa zabarsa da suka yi, tare da bayyana cewa zai ci gaba da ba su girmansu kamar yadda ya kamata.