✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dole PDP ta riƙa ɗaukar matakan da suka dace cikin sauri — Kwamitin Amintattu

PDP ta sha fama da rikice-rikice a baya-bayan nan kafin da kuma bayan faduwarta zaɓen Shugaban Kasa.

Jam’iyyar PDP ta amince da naɗa Sanata Adolphus Wabara a matsayin Shugaban Kwamitin Amintattun jam’iyyar.

Haka kuma jam’iyyar ta adawa ta amince da nada tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Sanata Ahmed Muhammad Makarfi a matsayin sakataren kwamitin.

Da yake jawabi jim kadan bayan nadin, sabon shugaban kwamitin na Amintattu ya bayyana a taron, wanda shi ne karo 76 cewa, za su yi aiki tukuru wajen dawo da martabar jam’iyyar domin hana yunkurin jam’iyyar APC na mayar da dimokuradiyyar kasar ta jam’iyya daya.

A cewarsa, “idan har Jam’iyyar PDP ta kwanta a Nijeriya, to lallai dimokuradiyyar kasar ce baki ɗaya za ta kwanta.”

Ya kara da cewa, kwamitin na amintattu aiki kawai zai fara babu kama hannun yaro domin fuskantar matsalolin da jam’iyyar ke fuskanta da siyasar kasar baki daya.

Ya bayyana cewa, daga manyan matsalolin jam’iyyar akwai rashin daukar matakan da suka dace a lokutan da suke dace, wadanda kuma hakan ke dawowa ya zama matsala ga jam’iyyar.

“Wasu mutane suna zargin mu da sakaci wajen daukar matakan ladabtarwa cikin lokaci a kan wadanda suka saba ko kuma suka yi ba daidai ba, lallai wannan maganar tasu tana kan hanya domin hakan na cikin abubuwan da suke jawo mana koma-baya a jam’iyyarmu.

“Muna duban sanayya wajen daukar matakan ladabtarwa. Amma wasu daga cikinmu, musamman mambobin kwamitin amintattu, babu ruwanmu da wannan.

“Muna kallon kowa a matsayin daya, kawai jam’iyyar ce a gabanmu. Don haka duk wani abu da ya saba wa dokokinmu na Kundin Tsarin Jam’iyyar da muka ga zai haifar da matsala, dole za mu magance shi.

“Dole mu rika duba abin da kundin tsarinmu ya nuna a kan duk wani abu da za mu yi, mu kasance masu amfani da dokar kasa da dokar jam’iyya. Idan muka yi haka, za mu samu nasara.”

A jawabinsa tun farko, Mukaddashin Shugaban Jam’iyyar PDP na kasa, Alhaji Umar Damagun ya tunatar da Kwamitin Amintattun cewa, aikin dawo da martabar PDP ya fi karfin Kwamitin Zartarwa kadai, inda ya ce ana bukatar sa hannun duk wani mai ruwa da tsaki a jam’iyyar domin ciyar da ita gaba da dawo da martabarta.

Daga cikin wadanda suka halarci taron akwai tsohon Gwamnan Jihar Jigawa, Sule Lamido da tsohon Gwamnan Jihar Imo, Emeka Ihedioha da Achike Udenwa na Imo da Babangida Aliyu na Neja da Ahmad Muhammad Makarfi na Kaduna da Donald Duke na Kuros Riba da sauransu.

Tun farko, Kungiyar Gwamnonin Jam’iyyar, karkashin jagorancin Gwamnan Jihar Bauchi, Sanata Bala Mohammed a wani taron da suka yi a Abuja, ta bayyana cewa akwai bukatar jam’iyyar ta duba tare da yin nazarin abubuwan da suka faru a jam’iyyar a baya-bayan nan tare da daukar matakan gyara da mayar da jam’iyyar a matsayin ta na babbar jam’iyyar adawa mai inganci.

Jam’iyyar PDP dai ta sha fama da rikice-rikice da ce-ceku-ce a baya-bayan nan kafin da kuma bayan faduwarta zaben Shugaban Kasa da Jam’iyyar APC mai mulki ta yi.

Haka kuma, ya biyo bayan dakatarwar da aka yi wa shugaban jam’iyyar na kasa, Sanata Iyorchia Ayu da masu ruwa da tsaki na jam’iyyar suka yi, wanda ya jawo ce-ceku-ce-da kuma yin kaca-kaca da wani jigo a jam’iyyar, Mista Segun Showunmi.

Hakan dai tasa tun a wancan lokaci ya garzaya kotu domin neman kwamitin zartarwa na jam’iyyar (NWC) ya nemi Hukumar Zabe ta Kasa da ta yi wa mambobinta karin haske, akan halin da jam’iyyar take ciki.

Wadanda suka halarci taron sun hada da Gwamna Bala Mohammed na Bauchi da Siminalayi Fubara na Jihar Ribas, Seyi Makinde na Oyo da Gwamna Ahmadu Umaru Fintiri na Adamawa, da kuma Caleb Mutfwang na Jihar Filatola da Dauda Lawal Dare na Zamfara, Kefas Agbu na Taraba, Godwin Obaseki na Jihar Edo da Mataimakin Gwamna Ifeanyi Ossai na Enugu da kuma Mataimakin Gwamna Jihar Delta Mista Monday John Onyeme.