#EndSARS: ‘Yan kabilar Ibo mazauna Kano sun ba Kanawa hakuri | Aminiya

#EndSARS: ‘Yan kabilar Ibo mazauna Kano sun ba Kanawa hakuri

Gwamna Ganduje tare da Mataimakinsa Gawuna
Gwamna Ganduje tare da Mataimakinsa Gawuna

Al’ummar kabilar Ibo mazauna Kano sun bawa gwamnatin Jihar Kano hakuri sakamakon hatsaniyar da ta auku kan zanga-zangar EndSARS da aka yi kwanan nan, wadda ta janyo asarar dukiyoyi da tsayar da al’amura.

Shugaban kabilar Ibo mazauna Kano, Igwe Boniface Igbokwe ya aike da wannan sako na rarrashin gwamnati da jama’ar Kano ga manema labarai a ranar asabar jim-kadan bayan kammala taron masu ruwa da tsaki da aka gudanar wanda Shugaban Karamar Hukumar Fagge, Alhaji Ibrahim Shehi ya jagoranta a kan batun zanga-zangar ta Kano.

Aminiya ta samu labarin zanga-zangar da aka gudanar a Kano a ranar Talata ta janyo asarar rayukan mutane 4 da kona ababen hawa kimanin guda 15, da lalata wasu gidajen mutane da awon gaba da kayayyakin mutane bayan an balle shagunan kasuwanci.

Shugaban kabilar Ibo mazauna Kano kuma shugaban kwamatin wanzar da zaman lafiya a jihar Kano Igbokwe, ya yi Allah-wadai da abin da matasan Ibo suka aikata a yankin unguwar Sabon Gari, ya kuma ce sam wannan ba dabi’ar mutanen su bace.

Shugaban ya ce “Sam ba zamu lamunci irin wannan shashanci da ayyukan ta’addanci makamancin wannan ba don wasu daga cikin masu zanga-zangar sun zo gidana da wasu kayayyakin sata da suka dauko sai na na kora su, nace bana goyan bayan wannan ta’addancin saboda Kano gari ne na zaman lafiya”.

Ya yi kira da hukumomin tsaro da su hukunta dukkan wanda aka samu da karya doka da oda.

A nasa jawabin Kwamishinan ’Yan sandan jihar Kano wanda ya samu wakilcin mataimakinsa mai kula da ayyuka, Balarabe Sule, ya ce hukumar ’yan sanda ta jihar Kano ba zata lamunci tayar da fitina da sunan zanga-zanga da zata hana gudanar da al’amuran yau da kullum kamar yadda aka saba a jihar Kano ba.