✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gara ta cinye takardun Naira biliyan 17 a Hukumar Kula da Inshorar Al’umma

Gara ta cinye takardun da ke fayyace musabbabin aika kudaden.

Hukumar Kula da Inshorar Al’umma a Najeriya (NSITF) ta ce gara ta cinye wasu takardu da ke kunshe da bayanan yadda ta kashe Naira biliyan 17.12.

Kafofin watsa labarai sun ruwaito NSITF na sanar da hakan ne ga Majalisar Dattawan Najeriya, inda ta bayyana cewa ba za ta iya fayyace bayanan kashe kudaden ba wanda ya zuwa yanzu babu duriyarsu.

A shekara ta 2018 ne rahotan binciken kudaden da aka kashe ya bayyana cewa, Asusun na NSITF ya yi amfani da bankunan Skye da First Bank wajen tura Naira biliyan 17.12 zuwa ga asusun bankunan wasu daidaikun mutane da kamfanoni daga watan Janairu zuwa Disambar shekarar 2013.

An dai gaza tantance ainihin makasudin aika makuden kudaden zuwa ga wadannan bankunan na daidaikun mutane da kamfanoni biyo bayan ikirarin NSITF na cewa, gara ta cinye takardun da ke fayyace musabbabin aika kudaden.

Ofishin Babban Mai Binciken Kudaden a Najeriya ya gabatar da tambayoyi 50 game da zarge-zargen barnatar da dukiyar kasa da hukumar ta NSITF ta yi, lamarin da yanzu haka ke gaban Kwamitinin Kula da Asusun Al’umma na Majalisar Dattawan kasar don ci gaba da bincike.

Kwamitin ya tuhumi tsoffin shugabannin NSITF da suka gabata da kuma na yanzu, amma babu wanda ya iya bayar da wani gamsasshen bayani.

Manaja Darektan NSITF na yanzu, Dokta Michael Akabogu ya bayyana cewa, babu wasu takardu mai nasaba da kudaden da ake bincike a kai da ya tarar a ofishinsa.