Gidan man minista ya kama da wuta | Aminiya

Gidan man minista ya kama da wuta

    Sagir Kano Saleh da Linus Effiong, Umuahiya

Gobara ta tashi a gidan mai mallakin kamfanin Master Energy da ke kan titin Aba a garin Umuahiya, hedikwatar Jihar Abiya.

Gidan man da ya kama da wuta yana kusa ne da wasu gidaje, daura da tsakiyar garin na Umuahiya, lamarin da ya sa mazauna unguwar yin gayya wajen taimaka wa jami’an kashe gobara domin ganin wutar ba ta yadu zuwa sauran gine-ginen da ke yankin ba.

Mazauna yankin sun ce gobarar da ta kama gidan man ta faro ne bayan wuta ta tashi daga wata motar dakon mai da take ajiye a harabar gidan man na Master Energy.

Kamfanin gidan mai din da ya kama da wuta mallakin minista mai ci a Ma’aikatar Tama da Karafa ne, Uchechukwu Sampson Ogah.

Mazaunan garin Umuahiya sun ce wutar ta shafe kimanin awa biyu tana ci a gidan man ban ba tare da jami’an hukumar kashe gobara sun yi nasarar shawo kanta ba.