✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gwamnati ta gabatar da sabbin kararraki kan Nnamdi Kanu

Sabbin tuhume-tuhumen kari ne a kan wadanda ake masa tun 2016.

Gwamnatin Najeriya ta shigar da sabbin tuhume-tuhume bakwai kan jagoran ’yan awaren Biyarafa, Nnamdi Kanu a gaban Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja.

Sabbin tuhume-tuhumen sun kushi cin amanar kasa da ta’addanci wadanda suka kasance kari a kan wadanda ake masa tun 2016.

Wakilinmu ya ruwaito cewa, Kotun ta sanya Alhamis, 21 ga watan Oktoba a matsayin ranar sauraron sabbin tuhume-tuhumen.

Tuni dai kotun da sanar da lauyan Kanu, Ifeanyi Ejiorfor a karar mai lamba FHC/ABJ/CR/383/15 da kuma mai gabatar da kara, Shuaibu Labaran.

Sanarwar ta nuna cewa, kotun karkashin jagorancin mai Sharia Binta Nyako ta yi sabbin umarni kan yadda za a gudanar da shari’a kan sabbin tuhume-tuhumen.

Duk wannan dai na zuwa ne yayin da Kungiyar Ohanaeze ta kabilar Ibo ta yi kira ga gwamnatin Najeriya a kan tabbatar da an mika Kanu kotu.

Ohanaeze ta ce gabatar da Kanu a kotu zai tabbatar wa duniya cewa yana cikin koshin lafiya kuma za a yi masa adalci a yayin shari’ar.

Tun a watan Yunin da ya gabata ne Babbar Kotun Tarayya ta ba da umarnin tsare Nnamdi Kanu a hannun hukumar tsaro ta DSS.

Ministan Shari’a, Abubakar Malami ne ya sanar da cewa a kasar waje jami’an tsaro suka cafko Nnamdi Kanu, bayan kotu ta bayar da belinsa domin kula da lafiyarsa

Malami ya bayyana wa ’yan jarida cewa a ranar Lahadi, 27 ga watan Yuni, 2021 ne hadin gwiwar hukumomin tsaron Najeriya suka cafke Kanu, aka kuma tiso keyarsa zuwa Najeriya.