✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gwamnatin Najeriya ta dakatar da tantance takardun digiri na jami’o’in Benin da Togo

Za mu toshe duk wata kafa da tare da ladabtar da jami’an da ke da hannu a irin wannan lamari.

Gwamnatin Tarayya ta sanar da ɗaukar matakin dakatar da tantance shaidar karatun digiri daga jami’o’in Jamhuriyar Benin da na Togo.

Wannan lamari dai na zuwa ne bayan wani rahoton binciken ƙwaƙwaf da Jaridar Daily Nigerian ta yi a baya-bayan nan, inda ta ce wani wakilinta da ya yi ɓad-da-kama ya samu takardar shaidar digiri daga wata jami’a a Jamhuriyar Benin a cikin mako shida kacal.

Rahoton ya fallasa yadda wani wakilin Daily Nigerian mai suna Umar Audu “ya kammala” digiri na shekaru hudu a kasa da watanni biyu daga Jami’ar Ecole Superieure de Gestion et de Technologies, ESGT, da ke Cotonou a Jamhuriyar Benin.

Sai dai a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun Ma’aikatar Ilimi ta Tarayyya, Augustina Obilor-Duru ya fitar, ya ce rahoton ya bayyana hanyoyin da wasu ’yan Najeriya ke bi domin samun takardar shaidar karatun digiri da nufin samun damamarmakin aiki da ba su cancanta ba.

A cewarsa, “Ma’aikatar Ilimi ta koka da irin wannan ɗabi’a kuma daga ranar 2 ga watan Janairun 2024, ta dakatar da tantance takardun shaidar karatun digiri daga Benin da Togo har zuwa lokacin da za a kammala bincike.

“Binciken dai zai haɗar da Ma’aikatar Harkokin Wajen Najeriya da kuma ƙasashen biyu da ma’aikatun da ke kula da ilimi a ƙasashen da kuma Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (DSS) da Hukumar Kula da Shirin Matasa Masu Hidimar Kasa, NYSC.”

Ma’aikatar ta yi kira ga ’yan Najeriya su ba da hadin kai wajen samar da bayanan da za su taimaka wa kwamitin yayin da yake neman hanyoyin magance faruwar haka a gaba.

Ma’aikatar ta kuma yi bayani kan ƙalubalen da take fuskanta game da matsalar bara-gurbin makarantun ƙetare ko a cikin gida waɗanda mutanen da ba su ji ba su gani ba, ke faɗawa tarkonsu ko kuma wasu ’yan Najeriya waɗanda da saninsu suke karatu a makarantun.

Ma’aikatar ilimin ta ce za ta ci gaba da nazari domin toshe duk wata kafa da hanyoyi da tsare-tsare tare da ladabtar da jami’an da ke da hannu a irin wannan lamari.