✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Har da ni a masu zuga Mbappe ya bar PSG — Ibrahimovic

Sai dai Zlatan ya ce zai zama wauta muddin PSG ta sayar da Mbappe.

Dan wasan kungiiyar AC Milan da Kasar Sweden, Zlatan Ibrahimovic ya tabbatar da cewa yana daya daga cikin mutane da suka zuga dan wasan PSG na Faransa Kylian Mbappe da ya bar kungiyar da ke taka leda a gasar Ligue 1 na Faransa.

A shekarun baya bayan nan an sha danganta dan wasan mai shekaru 22 da komawa Real Madrid, kuma Ibrahimovic ya yi imanin cewa lallai can zaifi dacewa da shi.

Da yake shaidawa jaridar wasanni ta Corrier dela Sera, Ibrahmovic ya ce “Mbappe na bukatar ingantaccen yanayi, kamar na Real Madrid.

Sai dai dan wasan na Sweden, wanda ya buga wa PSG wasanni 180, ya kuma shaida wa shugabannin kulob din na Faransa cewa zai zama wauta muddin suka sayar da Mbappe.

Mbappe ya koma kungiyar ne, a shekarar 2017 a matsayin aro, sai kuma daga baya ta kulla yarjeniniya ta dindindin da dan wasan.

Wasu dai na ganin cewa dauko Lionel Messi da kungiyar ta yi a wannan bazarar na daga cikin dalilan da suka sa Mbappe yake son barin kungiyar.

Madrid tana son sayo Mbappe a Janairu

Shugaban Kungiyar Kwallon Kafa ta Real Madrid, Florentino Perez, ya ce akwai yiwuwar kungiyar ta kulla yarjejeniya da Kylian Mbappe a lokacin da za a bude kasuwar hada-hadar ’yan kwallo a watan Janairun badi.

Shi kansa Mbappe ya ce ko a watan Janairu ya tuntubi kungiyarsa ta PSG da bukatar barin kungiyar, abin da yake nuni da cewa dan wasan ya kagara ya bar kungiyar.

Kylian Mbappe ya ce, da kansa ya nemi ya raba gari da PSG a daidai lokacin da Real Madrid take sha’awar sayensa a wannan kaka, duk da dai ya nanata cewa, yana jin dadin zama a birnin Paris.

Real Madrid ta yi tayin dan wasan mai shekara 22 a kan Fam miliyan 137, amma PSG ta yi watsi da tayin, yayin da ta sake yunkurawa, ita ma PSG din ta sake watsi da farashin.

Dan wasan ya ce, yana son komawa Real Madrid domin kauce wa tsarin nan na rabagari da PSG kyauta bayan karewar kwantaraginsa a kaka mai zuwa.

A cewar Mbappe yana son PSG ta samu kudi mai tsoka domin sayo wani kwararren dan wasa da zai maye gurbinsa.

Dan wasan ya ce, matsayarsa a bayyane take game da barin PSG.

Perez ya bayyana fatar cewa a ranar 1 ga Janairu za a yi ta ta kare game da batun kawo Mbappe Santiago Bernabeu.

A wannan kaka ce dai Real Madrid ta yi kokarin sayo Kylian Mbappe daga PSG ta Faransa, amma abin ya faskara, duk da cewa ta sanya wajen Yuro miliyan 170 a kan dan wasan gaban.

Ba zan zauna a PSG ba ko nawa za a biya ni — Mbappe

Shi kan shi Kylian Mbappe, ya ce ba zai rattaba hannu ba kan duk wani sabon kwataragi da kungiyarsa, Paris Saint Germain ta gabatar masa.

Mbappe ya ce ba zai sa hannu a sabuwar kwangilar ba ko da nawa kungiyar da ke buga gasar Ligue 1 za ta biya shi.

Kamfanin Dillancin Labaran wasanni na AS ya ruwaito dan wasan yana cewa, ba shi da wani buri face ganin yana murza leda a Real Madrid ta kasar Spain mai buga gasar La Liga.