✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Har yanzu Wike na fama da kuruciya – Sule Lamido

Ya ce ya kamata Wike ya dauki darasi daga Osinbajo da Peter Odili

Tsohon Gwamnan Jihar Jigawa, Alhaji Sule Lamido ya ce har yanzu kuruciya na damun Gwamnan Jihar Ribas, Nyesom Wike duk da kasancewar sa mutumin da ya san ya-kamata.

Yayin wata tattaunawarsa da Sashen Hausa na BBC a ranar Litinin, Sule ya ce akwai masu kokarin zuga Wiken wajen ganin ya yi wa jam’iyyarsa ta PDP zagon-kasa.

Gwamna Wike dai ya tsaya takarar Shugaban Kasa a PDP amma ya sha kaye a hannun Alhaji Atiku Abubakar a yayin zaben fid-da-gwanin jam’iyyar.

Gwamnan dai ya so ya zama Mataimakin dan takarar, amma Atiku ya dauki takwaransa na Delta, Ifeanyi Okowa, lamarin da bisa alama bai yi wasu da dama a cikin jam’iyyar dadi ba.

Sai dai Sule Lamido ya shawarci Wike da ya koyi darasi daga tsoho Gwamnan Ribas Peter Odili da Mataimakin Shugaban Kasa mai ci, Farfesa Yemi Osinbajo.

“Mun gudanar da Babban Taronmu na Kasa, wanda shi ne kololuwar masu fada a ji a jam’iyyar, kuma suka zabi Atiku. Wike ya tsaya takara amma bai yi nasara ba. Wike mutum ne da ya san ya-kamata, amma har yanzu akwai wani nau’i na kuruciya a tattare da shi.

“Akwai masu kokarin zuga shi, duk da cewa abin da zai faru ya riga ya faru, kuma wannan ba shi ne karon farko ba.

“A baya, haka ta taba faruwa da Peter Odili, sannan ta faru da Osinbajo, ya kamata ya dauki darasi daga wajensu,” inji shi.

Dangane da batun rikicin da ya tasamma kunno kai a PDP kuwa, Sule Lamido ya ce, “Ba laifi ba ne a samu baraka a cikin jam’iyya. Abu mai muhimmanci shi ne a sami mutane masu manufa da cancanta da za su magance matsalar.

“Ya kamata ’yan PDP su kwantar da hankalinsu don ba za mu ba su kunya ba, za mu magance dukkan matsalolin nan,” inji Sule Lamido.

Ya kuma ce zaben Gwamman da aka gudanar a jihar Osun a karshen mako wata ’yar manuniya ce da ke nuna alkiblar da ’yan Najeriya za su sa gaba a zaben 2023 mai zuwa.