✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Hatsarin jirgin ruwa ya yi ajalin manoma 20 a Kebbi

Jirgin ruwa mai dauke da manoman shinkafa kimanin 100 ya kife a cikin dare

Akalla manoman shinkafa 20 ake fargabar sun rasu sakamakon kifewar jirgin ruwa da dare a yankin Karamar Hukumar Koko/Besse da ke Jihar Kebbi.

Shugaban Karamar Hukumar Koko/Besse, Yahaya Bello, ya ce iftila’in ya auku ne a lokacin da jirgin ruwan ke dauke da manoma kimanin 100 a ranar Talata.

“Fasinjojom da lamarin ya shafa kusan baki dayansu matasa ne, maza da mata; Mun gano gawarwakin mutum 10, hudu mata da maza shida.

“Mun ceto kimanin mutum 80 kuma muna ci gaba da bincike domin gano sauran da suka bace,” in ji shi ga Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN), ranar Laraba.

Ya ce hatsarin ya auku ne a lokacin da manoman shinkafan ke kan hanyarsu ta zuwa kauyen Samanaji.

Shi ma dai kakakin ’yan sandan Jihar Kebbi, DSP Nafiu Abubakar, ya tabbatar da aukuwar iftila’in.