Hatsarin kwale-kwale ya kashe mutum 4 ’yan gida daya a Kebbi | Aminiya

Hatsarin kwale-kwale ya kashe mutum 4 ’yan gida daya a Kebbi

Masu aikin ceto bayan kifewar wani jirgin ruwa a Jihar Kebbi a shekarar 2021
Masu aikin ceto bayan kifewar wani jirgin ruwa a Jihar Kebbi a shekarar 2021
    Ishaq Isma’il Musa

Rahotanni sun bayyana cewa hatsarin kwale-kwale ya yi ajalin mutum 4 ’yan gida daya a Jihar Kebbi.

Hukumomi da mazauna yankin sun ce wadanda hatsarin ya rutsa da su suna hanyarsu ta zuwa gona tsallaken rafi ne.

Bayanai sun ce kwale-kwalen ya kife a ranar Laraba a yankin Yauri sakamakon iska mai karfin gaske.

BBC ya ruwaito cewa mutum shida ne ke cikin kwale-kwalen, wani uba Musa Labaran da ’ya’yansa.

Musa Labaran ya bayyana cewa an samu gawar ’ya’yansa hudu yayin da ake ci gaba da neman gawar mutum na biyar da ba a gani ba.

Ana iya tuna cewa a watan Mayun shekarar da ta gabata, sama da mutum 100 ne suka nutse a ruwa lokacin da kwale-kwalen da suke ciki ya kife a Jihar Kebbi.

Haka kum a cikin watan Disamba kimanin mutum 30 suka mutu a wani hatsari makamancin haka a Jihar Kano.

Ana danganta irin wannan al’amari ne da yadda ake loda wa kwale-kwale kaya da mutane da suka wuce kima da rashin kula da jiragen na ruwa da kuma rashin kyawun yanayi.