✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Hisbah ta kama mota maƙare da kwalaben barasa dubu 24 a Kano

Mun himmatu wajen aiwatar da manufar ba-sani-ba-sabo ga masu fasakwaurin barasa da sauran kayan maye.

Hukumar Hisbah ta samu nasarar kama wata babbar mota makare da kwalaben barasa sama da dubu 24 a Jihar Kano da ke Arewacin Najeriya.

Darakta Janar na hukumar, Abba Sufi ne ya bayyana hakan a wata sanarwa mai dauke da sa hannun jami’in hulda da jama’a na hukumar, Lawan Ibrahim Fagge.

Hukumar, wacce ta yi kamen barasar akan titin Zariya da ke Kano, ta kuma kama direban motar da karin wasu mutane biyu.

Sanarwar ta bayyana cewa an kama motar ce da tsakar daren ranar Litinin, inda take dauke da kwalabe daban-daban na barasa sama da 24,000.

Aminiya ta ruwaito cewa, an kwace motar daga hannun masu fasa kwaurinta domin daukar matakin da ya dace.

“Jami’an Hisbah a jihar sun himmatu wajen aiwatar da manufar ba-sani-ba-sabo ga masu fasakwaurin barasa da sauran kayan maye a cikin jihar,” in ji shi.

Ya kuma yi kira ga al’ummar jihar da su sanar da Hukumar Hisbah a duk lokacin da suka ga shige da ficen motocin da ke dauke da barasa musamman a kan titin Zariya da sauran manyan titunan da ke makwabtaka da jihar.