✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ina da koshin lafiyar da zan jagoranci Najeriya —Tinubu

Ku kalle ni da kyau, na yi kama da maras lafiya?

Dan takarar Shugaban Kasa na jam’iyyar APC Bola Ahmed Tinubu ya jaddada cewa yana da koshin lafiyar da zai iya shugabancin kasar nan.

Dan takarar ya bayyana haka ne a wani taron da ya yi da jiga-jigan jam’iyyar APC da kuma manyan ‘yan kasuwar Jihar Kano a ranar Asabar.

Tinubu ya musanta ikirarin da ake yi na cewa, ba shi da koshin lafiyar da zai iya mulkin kasar nan.

“Ba takarar tseren fanfalaki na ke yi ba, ko kuma takarar gasar kokawa na cin kambin duniya.

“Wadanda ke cewa ba ni da koshin lafiya, su kalle ni da kyau na yi kama da mara lafiya?” in ji Tinubu.

Dan takarar Shugaban Kasar ya yi wa kungiyar ‘yan kasuwar alkawarin idan an zabe shi, zai ba marada kunya, ta hanyar sauke duk alkawuran da ya dauka.

Aminiya ta ruwaito cewa, Tinubu ya sauka Jihar Kano tare da jiga-jigan jam’iyyar APC na Kasa da na jiha, da kuma gwamnonin jam’iyyar, inda ya kaddamar da yakin neman zabensa.

Kazalika, ya kaddamar da wasu ofisoshin yakin neman zabe, da kuma ganawa da wasu manyan masu fada-a-ji a jihar.