✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

INEC ta dage taron gaggawa kan zaben Adamawa zuwa ranar Talata

INEC ta ce ta dage tattaunawar ce domin wasu Kwamishinoninta su hallara

Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) ta dage taron gaggawar da ta shirya don yanke shawara a kan sakamakon zaben Gwamnan Jihar Adamawa zuwa ranar Talata.

Kwamishinan hukumar na kasa mai kula da wayar da kan masu zabe, Festus Okoye ne ya tabbatar wa Aminiya hakan a ranar Litinin.

Ya ce sun yanke shawarar dage ranar ce saboda a ba sauran Kwamishinonin hukumar da ke sauran Jihohi damar kammala ayyukansu domin su koma ranar Litinin su shirya wa tattaunawar kashegari a Abuja.

Tun farko dai INEC ta shirya taron ne domin tattaunawa a kan Kwamishinan nan nata na Jihar Adamawa, Farfesa Hudu Yunusa Ari, saboda abin da ta kira sanar da karashen sakamakon zaben Gwamnan Jihar ba bisa ka’ida ba.

Farfesa Hudu dai ya yi gaban kansa ne wajen sanar da ’yar takarar APC a Jihar, Sanata Aishatu Dahiru Binani, a matsayin wacce ta lashe zaben tun kafin a kammala tattara sakamakonsa.

Sai dai daga bisani hukumar INEC ta kasa ta soke ayyanawar da ya yi.

Idan za a iya tunawa, INEC ta ayyana zaben da aka gudanar a Jihar ranar 18 ga watan maris din da ya gabata a matsayin wanda bai kammala ba, sakamakon wasu sakamakon da ta sossoke saboda aringizon kuri’u da kuma rigingimu a yayin zaben.