✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Isra’ila ta kai sabon hari a Gaza

Ba a samu salwantar rayuka ba a sanadin harin.

Isra’ila ta kaddamar da hare-hare a kan “cibiyoyin soji” a yakin Gaza da maraicen ranar Asabar.

Wasu majiyoyin Falasdinu sun tabbatar da kai harin yayin da wasu majiyoyin rundunar sojin kasa na Isra’ila suka ce an kai hare-haren ne don mayar da martini bayan da wasu balo-balo masu dauke da ababe masu cin wuta suka haddasa gobara a wasu yankunan kasar a ‘yan kwanakin nan.

  1. An yi garkuwa da ma’aikata 8 a Kogi
  2. Biden ya yaba da yarjejeniyar tsagaita wuta a yakin Isra’ila da Falasdinawa

A cewar rundunar sojin ta Isra’ila, jiragen saman yaki sun “kai hari a kan wata cibiyar harhada makamai da wani wurin harba roka mallakar kungiyar Hamas”.

Kamfanin dillancin labarai na Faransa, AFP, ya ruwaito wasu majiyoyin tsaro da wadanda suka shaida faruwar lamarin a Gaza suna cewa an kai harin ne a kan wasu wurare a Yammacin Gaza da Zirin arewa.

Sai dai kuma ba a samu bayanan jikkata nan take ba.

“An kaddamar da hare-haren ne don mayar da martini ga balo-balo masu dauke da ababe masu kamawa da wuta da aka cilla zuwa yankunan Isra’ila”, inji wata sanarwa daga rundunar sojin kasa ta kasar.

Balo-balo din da aka tura daga Gaza dai sun tayar da wuta a yankin Eshkol na kudancin Isra’ila a ranakun Juma’a da Asabar, a cewar hukumar ’yan kwana-kwana.

Artabun watan Mayu

A ranar Alhamis ma an kashe wata wuta da ba ta kai ta kawo ba wadda balo-balo din daga Gaza suka tayar a wasu wurare a yankin na Eshokol.

Hakan ya sa Isra’ila ta kaddamar da hari da sanyin safiyar Juma’a wanda rundunar sojin kasar ta ce a kan “wata cibiyar kera makamai” mallakar Hamas aka kai.

Ranar 21 ga watan Mayu aka ayyana tsagaita bude-wutar da ya kawo karshen mummunan ba-ta-kashin da aka kwashe kwana 11 ana yi a tsakanin Isra’ila da Hamas da ma wasu kungiyoyi masu dauke da makamai a yankin na Gaza.

Har yanzu babu tabbas a kan kungiyar da ke kai hare-haren balo-balo din na baya-bayan nan daga yankin Gaza.

Balo-balon wuta

Tun bayan tsagaita bude-wutar dai ake ta aikewa da balo-balo masu tayar da gobara, lamarin da ke sa Isra’ila mayar da martini ta hanyar kai hare-hare ta sama.

Artabun na watan Mayu ya haifar da mutuwar Falasdinawa 260, ciki har da wasu mayaka, a cewar hukumomin yankin na Gaza.

A Isra’ila kuwa, mutum 13 aka kashe, ciki har da wani soja, a cewar ’yan sanda da rundunar sojin kasa.