✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Jarumin fim din ‘Fast and Furious’, Gibson, zai saki matarsa

Jarumin ya yanke wannan hukunci bayan shafe shekaru hudu da auren nasu.

Mawaki kuma Jarumin film din ‘Fast and Furious’, Tyrese Gibson ya bayyana aniyarsa ta raba aurensa da matarsa, Samantha Lee, bayan shafe shekaru hudu da aure.

Jarumin na Masana’antar Shirya Fina-finai ta Hollywood, ya bayyana hakan ne a shafinsa na Instagram ranar Alhamis, inda ya ce shi da matar tasa za su ci gaba da kasancewa abokan juna.

Ya kara da cewa a matsayinsa na bakar fata, rayuwarsa na cikin barazana a Amurka, dan haka ya yanke shawarar raba auren nasa.

Samantha, ita ce matar jarumin ta biyu, saboda a baya ya auri Norma Gibson tsakani shekarar 2007 zuwa 2009.

Sai dai jarumin bai bayyana dalilin da zai kawo rabuwar auren na su ba.

Amma ya ce kofarsa a bude take, domin a cewarsa ubangijin da suke bautawa zai gyara komai.