✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Jerin tafiye-tafiyen da Buhari ya yi zuwa ketare a bana

Sai babu shakka tafiye-tafiyen da shugaban ya saba yi sun ja baya bayan bullar annobar Coronavirus.

’Yan Najeriya na ci gaba da bayyana damuwa dangane da tafiye-tafiyen da Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ke yi zuwa ketare babu kakkautawa ba.

Wasu dai na zargin cewa, tafiye-tafiyen da Buharin ke yi ba sa kawo wa kasar nan wata fa’ida a zahiri ba kamar yadda rahoton jaridar Daily Trust na ranar Lahadi ya zayyana.

Galibi dai, shugabannin kasasashe kan yi balaguro zuwa ketare domin halartar wasu muhimman al’amura, inganta alakar diflomasiyya ko kulla wata yarjejeniyar kasuwanci tsakanin kasashe.

Ya zuwa yanzu tun bayan hawansa kujerar mulki shekaru bakwai da suka gabata, jama’a na ci gaba da sukar Shugaba Buhari kan yawan tafiye-tafiyen da yake yi zuwa kasashen ketare, inda masu sukar ke zargin cewa yana amfani da kudin baitul mali ba tare da wata fa’ida ba.

Wasu kuma na sukar shugaban kasar kan yadda yake fifita tafiye-tafiyensa zuwa ketare a kan yinsu a cikin gida, wanda a cewarsu hakan zai ba shi damar tunkarar matsalolin da suka shafi kasa baki daya.

Sai babu shakka tafiye-tafiyen da shugaban ya saba yi sun ja baya bayan bullar annobar Coronavirus wacce ta bude kofar halartar halartar tarurruka daga nesa tsawon shekaru biyu.

Sai dai kuma bayan sassauta dokar hana tafiye-tafiye da annobar Coronavirus ta janyo, shugaba Buhari ya koma kan ganiyarsa ta ci gaba da tafiye-tafiye daga wannan kasa zuwa waccan.

Ga jerin tafiye-tafiyen da Buhari ya yi zuwa ketare a bana

A rubu’i na biyu na shekarar 2022, binciken jaridar Daily Trust ya nuna cewa shugaba Buhari ya yi balaguro zuwa kasashen ketare guda goma.

Tafiyar baya bayan nan da Buharin ya yi ita ce ziyarar da ya kai kasar Portugal a makon jiya, inda ya gana da Shugaba Marcelo Rebelo de Sousa. Ya kuma halarci taron Majalisar Dinkin Duniya na United Nations Ocean Conference daga ranar 27 ga Yuni zuwa 1 ga Yuli a Lisbon, babban birnin kasar.

Gabanin wannan balaguro, shugaba Buhari ya halarci taron Kungiyar Kasashe Renon Ingila karo na 26 (CHOGM), wanda aka gudanar daga ranar 20 zuwa 26 ga watan Yunin 2022 a birnin Kigali na kasar Rwanda

Haka kuma, a ranar 4 ga watan Yuni, shugaban ya halarci wani babban taro na musamman na Shugabannin Kasashen Yammacin Afirka (ECOWAS) kan harkokin siyasa a kasar Mali da sauran sassan yankin a birnin Accra na kasar Ghana.

A ranar 1 ga watan Yuni, Buhari ya tafi ziyarar aiki ta kwanaki biyu a Madrid, babban birnin kasar Spain, bisa gayyatar takwaransa na Spain, Pedro Sanchez.

A watan Mayu kuma, shugaba Buhari ya ziyarci Masarautar Hadaddiyar Daular Larabawa domin jajanta wa kasar bisa rasuwar tsohon shugabanta, Sheikh Khalifa bin Zayed Al-Nayan.

A watan Mayun dai, Buhari ya ziyarci Equatorial Guinea, inda ya halarci babban taron Kungiyar Tarayyar Afirka; da kuma kasar Kwaddebuwa (Ivory Coast), inda ya halarci taron Majalisar Dinkin Duniya karo na 15 kan yaki da hamada.

Shugaban ya kuma ziyarci birnin Brussels na kasar Belgium a watan Fabrairu, inda halarci taron kungiyar Tarayyar Turai da Tarayyar Afirka karo na 6.

A watan Maris ne Buhari ya ziyarci Nairobi, babban birnin kasar Kenya, don halartar bikin cika shekaru 50 da kafa Hukumar Kula da Muhalli ta Majalisar Dinkin Duniya.

A cikin watan Maris din dai, Buhari ya kai ziyarci ganin Likita a birnin Landan na kasar Birtaniya, inda ya shafe makonni biyu yana jinya.

Tun a watan Fabrairu kuma Buhari ya ziyarci birnin Addis Ababa na kasar Habasha domin halartar taro karo na 35 na Majalisar Dinkin Duniya da shugabannin kasashe da gwamnatocin Tarayyar Afirka.