JIDALIN KISHIYA: Labarin Farida (21) | Aminiya

JIDALIN KISHIYA: Labarin Farida (21)

    Bashir Yahuza Malumfashi

A ci gaba da wannan labari, a makon jiya mun tsaya ne daidai inda aka ce: “Subhanallahi! Ta yaya kika banzatar da kanki haka?” Binta ta wangale baki, ta kura wa kawarta ido cikin mamaki da kaduwa.” Ga ci gaba:

Kawayen biyu sun dauki kimanin minti biyu ba su furta komai ba. Binta, baki a wangale tana mamakin yadda aka yi kawarta ta biye wa rudin namiji har ya dirka mata ciki, a yayin da ita kuma Saratu ta kasance cikin kunar rai. Bayan sun samu damar ci gaba da magana ce ta ci gaba da kwance mata zaren labarin matsalarta.

“Tunda farko matsala ce ta hada ni da Malam Dandauda, kasancewarsa malaminmu na Ingilishi a jami’a. An samu lokacin da na samu matsala, na fadi jarrabawar zangon karatu a darasin da yake koya mana. Wata ’yar ajinmu ce ma ta hada ni da shi.”

“Ta hada ki da shi kamar yaya?” Binta ta bijiro mata da tambaya.

A kan haka ne Saratu ta sanar da ita cewa a ranar da ta sanar da ’yar ajinsu matsalarta, shi ne ta ba ta shawarar cewa ta je ta samu Malam Dandauda, zai taimaka mata. Ta ce mata yana da kirki, ita ma wai ta taba samun irin wannan matsalar kuma ya taimaka mata.

“Yarinyar nan ta boye mini wani abu, wato ba ta sanar da ni cewa mazinaci ba ne shi. Lokacin da na same shi a ofis, bayan na yi sallama ya ce in shiga. Ina shiga ya dago kai ya kalle ni, fuskarsa rufe da wani fankacecen tabarau. Ya bude bakinsa kadan ya saki wani murmushi, tare da bayyanar da wata siririyar wushirya.”

A lokacin da Saratu ta fadi haka, Binta ta lura da yadda jikinta ya yi sanyi, murtukakkiyar fuskarta ta saki, alamar da take nuna yadda shaukin soyayya ya motsa a ranta.

“In gaya miki gaskiya, tun daga lokacin nan na ji ya zauna a zuciyata.” Saratu ta ci gaba da labarinta. “Dandauda mutu ne mai kwarjini, yana da wuya mace ta hada ido da shi ba ta ji wani shauki ya shige ta ba. Muryarsa ma kadai tamkar wani maganadisu ne da ke tattare da albishir din jawo ra’ayi.”

Saratu ta shaida wa kawarta yadda cikin saukin kai da kalamai masu dadi ya amshe ta. Lokacin da ta sanar da shi irin matsalar da ta kawo ta, ba tare da bata lokaci ba ya ce ta kwantar da hankalinta. Ya mika mata wata gajeruwar takarda, ya ce ta rubuta sunanta, lambar kwas dinta da kuma lambar wayarta.

“Lokacin da na yi ban-kwana da shi, na kama hanya zan fita daga ofishinsa, har na yi taki biyu, na kusa zuwa kofa, sai ya kirawo ni. Bayan na waigo sai na ga ya miko mini kudi, ya ce in biya kudin tasi. Na yi kokarin cewa ba zan amsa ba sai ya bude baki cikin murmushi. Ya ce idan ba rainawa na yi ba, in amsa. Ni kuwa na amsa na yi godiya sannan na fita daga ofishin cike da annashuwa da farin ciki. Babban farin cikina shi ne yadda na ga alamar cewa lallai matsalata ta kawo karshe.”

“Ki ce ashe labarin da tsawo,” inji Saratu.

“In gajarce miki labari, iyaka batun ke nan, domin kuwa tun daga ranar ya fara kiran wayata da dare. Daga karshe ya ce mini yana da kyau ya rika shirya mini lacca ta musamman, domin in rika fahimtar kwas dinsa.” Saratu ta fashe da kuka, sai da kyar Binta ta sake lallashinta, ta sake samun natsuwa.

“Kawata, ba zan taba mance ranar nan ba.” Ta fadi haka tana cikin shesshekar kuka.

“A ranar farko da na fara zuwa daukar darasin nan a gidansa, a ranar ce kuma ya yaudare ni, ya kawar mini da mutuncina, ya lalata mini budurcina!” Ta sake fashewa da kuka.

“Haba, don Allah ai ba kuka za ki yi ba. Kamata ya yi ki kwantar da hankalinki, mu ci gaba da laluben mafita kawai amma ai kuka ba zai magance miki matsalar nan ba, sai ma karin takaici!” Binta tana magana cikin damuwa da bacin rai. Ta kalli Saratu ta ga yadda duk ta sukurkuce, tausayinta ya kama ta. “To, idan ban yi kuka ba me zan yi? Wallahi zubar hawayena, shi ke danne mini kullutun bakin ciki, shi ke hana ni jin zafin takaici da bakin tunanin da ke bijiro mini. A duk lokacin da na tuno da ranar nan, ji nake kamar in kashe kaina.” Ta yi doguwar ajiyar zuciya tare da shessheka.

“Yanzu ne na tuno da nasihar da wani malami ya taba yi mana. Abi da ya fada mana gaskiya ne. Ya ce budurcin ’ya mace shi ne babban arzikinta, shi ne rayuwarta, shi ne sirrinta kuma shi ne diyaucinta. Matukar ba mijinta na aure ne ya cire shi ba, to mace za ta kasance cikin takaici har karshen rayuwarta. Macen duk da ta yi asarar budurcinta a rariya, ta yi wa zuriyarta tabo, tun daga danta na farko har zuwa tattaba kunnenta na karshe. Gaskiya na cuci kaina, na cuci zuriyata, ba zan taba yafe wa Dandauda ba!” Saratu ta kara yin shiru, a lokacin da Binta ta ma rasa abin da za ta fada mata.

Za mu ci gaba