✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Sakamakwon Zaben Gwamnonin Najeriya Na 2023 (Alkaluma Daga:INEC)

Kabiru Rurum ya ci zabe bayan komawarsa NNPP

Kabiru Alhassan Rurum, tsohon Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Kano ne kafin ya zama dan Majalisar Tarayya.

Dan Majalisar Tarayya mai wakiltar Rano/Kibiya/Bunkure a Jihar Kano ya yi nasarar lashe zabe bayan sauya sheka daga APC zuwa NNPP.

Kabiru Alhassan Rurum, tsohon Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Kano ne kafin ya zama dan Majalisar Tarayya.

Jami’in bayyana sakamakon zabe, Farfesa Suleiman Yusuf Mudi ya sanar cewa jam’iyyar NNPP ta samu kuri’u 50,160.

Jam’iyyar APC ce ta zo ta biyu kuri’u 35,235 yayin da PDP ta samu 2,234.